Connect with us

Labaran Najeriya

Bayanin Shugaba Muhammadu Buhari kan Bikin Eid-Maulud

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar 10 ga Nuwamba, watau Lahadin da ta gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi musulman kasar nan da su nisanci munanan ayyukan da suka sabawa koyarwar da kwatanci da rayuwar Annabi Muhammadu.

Naija News Hausa ta fahimci cewa shugaban ya fadi hakan ne a yayin da yake bada jawabi a cikin sakon fatan alheri da aka bayar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, na bikin Maulud don tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad.

Shugaban a cikin bayanin sa ya ce bukaci a guje wa kisa ga mutanen da ba su aika wata laifi ba, sace dalibai mata da tilasta su ga aure da juyiya wajen koyarwa da misalai da suka saba wa ta Annabi Muhammadu.

Buhari ya bayyana da cewa tsattsauran ra’ayi da mugunta daga wasu mutane da ke amfani da addini wajen aikata mumunan ayuka don dakile ka’idojin laifinsu na haifar da babban kalubale ga sunan addinin Musulunci. Ya kuwa bukaci musulman kasar nan da su dakatar da yaduwar akidu wadanda ke haifar da bala’i a kasar.

Shugaban ya shawarci musulmai a fadin kasar da kar su yi watsi da kyale ‘ya’yansu ga hannun mutanen da za su iya koyar da su a halin da bai dace ba. Ya kuma taya musulmai murnar da fatar alhairi ga hidimar Maulud da ake ciki da kuma shawartan su da su yi amfani da wannan bikin don sabunta niyyarsu ta inganta, kauna da samar da zaman lafiya a kasar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Lauyan kundin tsarin mulki da kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shirin neman sake komawa ga mulki a wa’adi na uku a shekara ta 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa wasu kungiyoyi na kira ga shugaba Buhari da ya tsawaita da shugabancinsa har ga shekarar 2023.