Connect with us

Uncategorized

Eid-Ed Maulud: Karanta Sabuwar Sakon Atiku Abubakar ga ‘Yan Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar a ranar Lahadin da ta gabata ya bukaci Musulmai da su yi amfani da addini don tabbatar da kauna, kwanciyar hankali, hadin kai da fahimta a kasar Najeriya.

Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (2019) a zaben 2019 ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta sanar a baya da cewa musulmai a kasar ranar Litinin, 11 ga Nuwamba 2019, zasu yi bikin Maulud domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad.

A cewar Atiku, Addini wani abu ne da ake bukata don zaman lafiya da kwanciyar hankali ya gudana a kasa.

Ya kuwa yi kira ga shugabannin addinai da su yi amfani da matsayinsu mai tasiri don yada soyayya, hakuri da girmamawa ga wasu wadanda suka bambanta a addininsu.

Ya kara da cewa; “Annabi Muhammadu abin dubi ne ga kwatancin zaman lafiya, kaskantar da kai da adalci ga kowa, kuma kamar yadda muke girmama shi a wannan babban biki, bari mu bi sawunsa cikin kalamai da ayyukansa.” inji Atiku.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya kuma yi kira ga shugabannin musulmai da su kara himma wajen yaki da kishin addini wanda ke da sanadiyar wasu manyar kiyayya da tashe tashen hankula a kasar.

KARANTA WANNAN KUMA; Fati Washa Ta Karbi Karin Girma Na Kyautar Gwarzuwar Jaruma a Birtaniya