Connect with us

Uncategorized

Kogi: Gobara ta Afka da Kone Sakatariyar Jam’iyyar SDP a Jihar Kogi

Published

on

at

Rahotanni da suka iso ga Naija News ya bayyana da cewa an kona sakatariyar Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar rahoton da wakilinmu ya tattara, mutane da ba a san ko su wanene ba amma da ake zargi da zaman ‘yan tada zama tsaye wajen hidimar siyasa, sun kutsa cikin sakatariyar jam’iyyar SDP da sanyin safiyar ranar Litinin, suka kuma kone ofishin kurmus.

Al’amarin ya faru ne kwanaki biyar kacal ga hidimar zaben kujerar gwamnan jihar, wadda hukumar INEC ta sanar da gudana a ranar 16 ga Nuwamba a jihar.

Kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta ruwaito a baya da cewa an kai wata hari kan sakatariyar SDP a ranar Lahadin da ta gabata.

An bayar da cewa an lalace dukan kofofin sakatariyar, yayin da aka kuwa lalata wasu kayan hidimar neman zabe tare da musanya wasu da fostocin dan takarar jam’iyyar APC, Yahaya Bello.

Jam’iyyar SDP ta zargi jam’iyyar APC da wata shirin kai hari kan ayarin dan takarar gwamna a jam’iyyar  SDP, Natasha Akpoti da neman sace ta.

Ku tuna da cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, ta umarci Hukumar gudanar da hidimar zabe (INEC) da ta maido da Madam Natasha Akpoti, ‘yar takara a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna na ranar 16 ga Nuwamba mai zuwa a jihar Kogi.

KARANTA WANNAN KUMA; Idan ba za ku iya ciyar da Iyalanku ba, to kada ku tura yaranku don yin bara a Madadin ku – inji Sarkin Kano.