Connect with us

Uncategorized

Idan ba za ku iya ciyar da Iyalanku ba, to kada ku tura yaranku don yin bara a Madadin ku – inji Sarkin Kano

Published

on

at

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, a ranar Asabar din da ta gabata a yayin wata gabatarwa ya nemi a jefa iyayen yaran da aka sace a Kano ga gidan yari saboda watsi da yayansu da ke yawo a tituna.

Ka tuna an ruwaito a labarai a ranar 12 ga Oktoba da ta wuce, da cewa rundunar ‘yan sanda ta Kano ta sanar da ceton wasu yara tara da aka sace a cikin garin Kano da safarar su zuwa Onitsha a jihar Anambra.

Rahoton sace yaran ya haifar da jita-jita a da har ya kai Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin bincike a kan lamarin wadda shugaban, Jama’atu Nasrul Islam, kungiyar Kiristocin Najeriya, kungiyoyin kare hakkin Al’umma duka suka yi Allah wadai da ita.

A yayin magana a cibiyar Affanuwa a Kano, lokacin taron yaki da yin amfani da miyagun kwayoyi wanda kungiyar kula da Lafiya (LESPADA) ta shirya, Sarkin Kano ya ce iyayen yaran da aka sace sun cancanci a tuhume su da laifin sakaci.

“Game da batun yaran da aka sace a Jihar Kano, na riga nayi magana da Obi, sarkin Iyamirai ta Onitsha kan zancen. Muna kuma sa ido kan lamarin.”

“Kwarai da gaske mun ji cece-kuce da ke tasowa a kan Iyamirai cewa an sace yaranmu. Shin in tambayeku, ‘yan Igbo masu satar mutanen sun shiga gidan ku don sace yaran? Ko ko dai, kun ƙyale ɗiyanku da yawo a tituna da gangan?”

Dole ne mu fada wa kanmu gaskiya. A lokacin da iyaye suka fara gabatar da karar yaransu da suka bata, na ce, idan da ace ina da karfin kaina, da na tura iyayen a gidan yari.

“Na ba da umarnin a tambayi kwamishinan ‘yan sanda idan muna da wata doka da ake kera ga laifin sakaci. Shin bamu da irin wannan dokar ne? Duk wanda yazo da rahoton cewa an sace diyansa da akalla shekaru 4 yayin wasa ya cancanci a daure shi. Sakaci da laifi!

“Mu Hausawa ya zan dole mu canza tunaninmu. A koyaushe za mu ɗora alhakin laifi akan Igbo, Yarabawa, a yayin da kuwa laifinmu ne.”

“A yanzu, yi yunƙurin sace a Onitsha ka gani ko da zaka ci nasara da kama daya. Shin wannan ba gaskiya bane? Shin sun bar yaransu ‘yan shekaru 3 zuwa 4 suna yawo a titi suna bara kamar mallam bahaushe?

“Idan ba za ku iya ciyar da danginku ba, to, kada ku tura yaranku don yin bara a madadinku. Idan muka ci gaba da rayuwa ta musunmu, zamu kuwa yi kuka nan gaba bayan zargin wasu.”

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa na ke kwanci da Maza 15 a kowace Rana – Wata ‘Yar Shekara 15