Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 11 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 11 ga Watan Nuwamba, 2019

1. 2023: Falana Ya zargi Buhari da Shiryawa Batun Neman Takara a Karo na 3

Lauyan kundin tsarin mulki da kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shirin neman sake komawa ga mulki a wa’adi na uku a shekara ta 2023.

Advertisement
Advertisement

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa wasu kungiyoyi na kira ga shugaba Buhari da ya tsawaita da shugabancinsa har ga shekarar 2023.

Advertisement
2. Fashola Ya Mayar da Martani Game da Kalamunsa a kan hanyoyin Najeriya

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya ce anyi rashin fahimtar jawabin da ya yi kan hanyoyin manyan hanyoyin tarayya a fadin Najeriya.

Advertisement
Advertisement

Naija News ta tuno da cewa Fashola ya bayyana a baya da cewa yawar ikirarin da ake yi akan lalacewar hanyoyin kasar Najeriya ba gaskiya bane duka.

Advertisement
3. Sojojin Sama sunyi Karin Girma ga wasu Manyan Hafsoshi

Kwamitin Rundunar Sojin Sama (AFC) ta Najeriya a ranar Lahadi ta amince da gabatar da karin girma ga manyan hafsoshin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF).

Advertisement

An sanar da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar daga bakin Daraktan hulda da jama’a da watsa labarai na rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore, Ibikunle Daramola.

Advertisement
Advertisement
4. NGF ta Mayar da Martani kan Musanta katin Fita kasar waje ga Gwamna Fayemi

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta karyata rahotannin da ke nuna da cewa ofishin jakadancin Ameriya a Najeriya ta hana gwamna Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti katin tafiya zuwa kasar waje.

Advertisement

Wani dandamali ta yanar gizo (amma ba News News ba), ta yi ikirarin cewa an hana Fayemi, Shugaban NGF izinin shiga Amurka.

Advertisement
5. 2023: Babu Tabbaci ga Shugabancin Igbo, Arewa na iya sake Takara – Gulak

Tsohon mai ba da shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan al’amuran siyasa, Ahmed Ali Gulak, ya ce neman shugabancin kasa ga Igbo ba shi da tabbas kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Advertisement
Advertisement

Gulak da yake bada jawabi ga manema labarai ta The Sun, ya ce, rabar da shugabanci a yankunan kasa ba ya cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma Peoples Democratic Party (PDP).

Advertisement
6. Akpabio: Ekpenyong ya Mayar da Martani dangane da Cin Nasara a Kotun daukaka kara

Sanata Chris Ekpenyong ya mayar da martani game da kayen da ya sha a hukuncin Kotun daukaka kara ta Ministan Harkokin Neja Delta, Sanata Godwill Akpabio.

Advertisement

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Kotun daukaka kara da ke zaune a Calabar ta soke zaben Dr Chris Ekpenyong, na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma ta yanke hukunci a kan Sen. Godswill Akpabio, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa.

Advertisement
Advertisement
7. Buhari: Atiku ya mayar da martani kan Asarar shugabancin kasa da yayi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya caccaki fadar shugaban kasa da kalamai saboda yin ba’a da asarar da ya yi a Kotun Koli.

Advertisement

Naija News ta rahoto cewa mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina a cikin wata sanarwa a ranar Asabar ya bada jerin wasu mutane da suka “yaudari” Atiku ba bashi tabbacin cewa zai zama shugaban kasa.

Advertisement
Advertisement

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
Advertisement