Connect with us

Labaran Najeriya

Mutuwa Rigan Kowa: Shugaba Muhammadu Buhari Yayi Rashin Abokin sa, Tam David-West

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News ta samu rahoton mutuwar dan shekara 83, Farfesa Tam David-West, babban mai goyon baya ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

Wannan gidan labarai na da sanin cewa Mista David West ya yi jagoranci a matsayin ministan man fetur da makamashi a karkashin gwamnatin mulkin soja ta Muhammadu Buhari, da kuma yin Ministan ma’adanai, Wuta da Karfe a karkashin mulkin Janar Ibrahim Babangida, a shekarun da suka gabata.

Shugaba Buhari ta hannun mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina ya bayyana marigayin a matsayin mutumi mai karfin hali da zuciya, mutumi mai dagewa ga duk abinda ya yi imani da shi, kuma da kasancewa a cikin tsarinsa.

Shugaba Muhammadu Buhari Ya yi gaisuwar ta’azziya ga dangin David-West, da mutanen Bayama, Kalabari da masarautar Kalabari, da kwaleji, da duk wadanda ke kauna da “madaidaiciyar Tam David-West.”

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya hutar da mamaicin, mutumi mai kishin kasar nan kwarai da gaske. Ya kuma roki dukkan al’umma da su kasance da imani da manufofin da ya dace, don ci gaban Najeriya, da kuma bil’adama baki daya.