Connect with us

Uncategorized

Yadda Aka Kunyatar da Gwamna Yahaya Bello a Kogi (Kalli Bidiyo)

Published

on

at

advertisement

Wani faifan bidiyo da kamfanin dilancin labarai ta Naija News Hausa ta gano a layin sada zumunta ya nuna lokacin mutanen Kogi suka kunyatar da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, arewa maso-tsakiyar Najeriya.

Naija News ta fahimci cewa an kunyata Gwamnan ne a yammacin ranar Lahadi, 10 ga Nuwamba a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cikin faifan bidiyon wanda aka rabas ta shafin yanar gizon Twitter a hannun Sanata Dino Melaye, yayi nunin yadda mutanen Lokoja suka yiwa gwamna tsuwa da zage-zage a lokacin da ayarin motocin sa suke wucewa ta hanyar Lokoja.

A cikin bidiyon mai tsawon mintina 2 wanda Naija News ta gano, za ka iya jin mutanen Kogi suna tsuwa da kiran sa “Ole…. Ole”, ma’an ‘barawo… barawo’, a yayin da gwamnan ke wucewa.

“Ku kalli yadda ake yiwa Yahaya Bello tsuwa da zagi a yayin da yake zagayar Jihar Kogi” inji Sanata Melaye, dan majalisa a dandamali na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da kuma babban mai sukar gwamna Bello, a yayin rabar da bidiyon a shafin Twitter.

Kalli bidiyon a kasa kamar yadda Dino Melaye ya rabar;