Connect with us

Uncategorized

2023: Balarabe Musa yayi Magana kan Abinda Zai Faru Idan Nigeria Ta Rabu

Published

on

at

advertisement

Wani tsohon gwamnan jihar Kaduna, Abdulkadir Balarabe Musa, ya bayyana da cewa idan har Najeriya ta rabu, wannan ba zai kawo karshen matsalolin da kasar ke fuskanta ba.

Ya lura da bayyana da cewa yankunonin kasar zata ci gaba da fama da irin wadannan matsalolin da ake kokarin tserewa.

Balarabe a cikin bayaninsa da manema labarai ya fada da cewa ya kamata a canza duk shugabancin siyasa da tsarin da bai daidaita ba.

“hanya daya tilo da za a iya magance matsalolin kasar nan ita ce kawai a canza tsarin zamantakewa, siyasa da tattalin arziki da suka dakile dukkan ci gaba mai kyau a kasar” inji shi.

“haka Najeriya take ci gaba. Ba za ku iya yin komai game da wannan ba saboda wannan tsarin ya haifar da jagoranci wanda ba shi damu ba da lafiyar mutananta.”

Ya ce tsarin kasar kawai ta damu ne da ci gaba da mulki da kuma kara yin muni ga matsalolin da ta kirkiro da kanta.

Dattijon ya lura cewa kowa na bin kawai ne hanyar kudi, yadda zai ci gaba da kwasar kuɗi da kuma nuna iko.

“Hanya guda daya tilo ita ce canza tsarin shugabancin da siyasar da kasar ta samar.”