Connect with us

Uncategorized

Sabuwar Labari: Kotu ta Kori dan takarar gwamnan jihar Bayelsa na APC

Published

on

at

advertisement

Rahoto da ke isa ga Naija News Hausa a wannan lokaci ya bayyana da cewa babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a yau Talata, 12 ga Watan Nuwamba ta hana mataimakin dan takarar gwamna a jihar Bayelsa daga jam’iyyar All Progressives Congress, Biobarakuma Degi, shiga tseren takara a ranar Asabar mai zuwa, 16 ga Nuwamba, 2019, a zaben gwamna a jihar.

Hakan ya bayyana ne daga bakin Mai shari’a Inyang Ekwo, a yayin da yake gabatar da hukunci a karar wacce aka yi da lambar shaida FHC / ABJ / CS / 1101/2019, wadda jam’iyyar Peoples Democratic Party da sauran ‘yan jam’iyu suka kafa gabatar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa an kona sakatariyar Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar rahoton da wakilinmu ya tattara, mutane da ba a san ko su wanene ba amma da ake zargi da zaman ‘yan tada zama tsaye wajen hidimar siyasa, sun kutsa cikin sakatariyar jam’iyyar SDP da sanyin safiyar ranar Litinin da ta wuce, suka kuwa kone ofishin kurmus da wuta.

Al’amarin ya faru ne ‘yan kwanaki kadan ga hidimar zaben kujerar gwamnan jihar, wadda hukumar INEC ta sanar da gudana a ranar 16 ga Nuwamba a jihar.