Connect with us

Uncategorized

An Gano Dan Shekaru 11 Da Aka Sace a Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoto da ke isa ga Naija News Hausa ya bayyana da cewa an gano wani yaro dan shekaru 11 da aka sace a jihar Kano a shekarar 2014.

Wannan kamfanin Dilancin labarai ta fahimta da cea an sami yaron ne a jihar Anambra bayan bincike na tsawon shekaru 5.

An ci nasara ne da gano yaron mai suna Muhammed Ya’u, bayan gwagwarmaya da zagayar bincike da rukunin Operation Puff Adder ta ‘yan sandan reshen jihar Kano ta yi. Bayan shekaru 5 da aka sace yaron a shiyar PRP Quarter a Kano ta hannun wani mai suna Paul Onwe da Matarsa Mercy Paul wanda suka sace shi tare da siyar shi kuma ga wani mai suna Ebere Ogbodo a kimanin kudi naira dubu N200,000.

Rahoton ya bayyana da cewa wadanda suka sayeshi sun canza masa suna zuwa Chinedu Ogbodo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya bada tabbaci ga faruwar lamarin kuma ya kara bayyana cewa an kama mutane uku a haka.

“A ci gaba da kokarin da rundunar mu ta yi na kubutar da yaran da aka sace daga Kano zuwa wasu sassan kasar nan, tsakanin 05/11/2014 zuwa 08/11/2019, rukunin rundunar ta Anti Kidnapping Team of Operation Puff Adder ta sake yin wani zagaye.”