Connect with us

Uncategorized

Gobara Ya Lashe Shashen Gidan Gwamnatin Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda Gobara ta kame ofishin Sakataren dindindin na gidan gwamnatin jihar Neja, sakamakon hadewar wayar wutar lantarki.

Rahoto ya bayar da cewa ya kame ne da gobara a yayin da ake kan aiki da gyara gidan gwamnatin. Gobarar ya dauki sama da mintuna 15 kafin wasu ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar suka isa wajen don tsayar da gobarar da yaduwa.

A bayanin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), an gano ma’aikatan Ofishin suna gudu don tsira da rayukansu kafin ma’aikatan hukumar kashe gobara suka isa da manyan motoci uku a wajen.

Sun bayyana da cewa kayan aiki na ofishin, masarufi da takardu masu mahimmanci duk sun kone a cikin gobarar.

Mataimakin shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Neja, Malam Salihu Bello, a yayin zanta da manema labarai ya bayyana da cewa saurin isar ma’aikatan kashe gobarar ya taimaka kwarai da gaske wajen rage munin alamuran.

Ya fada da cewa rashin manyan motocin kashe gobara a gidan gwamnati ba da niyya ba ne yayin da ake shirin tsaida daya a wajen don saurin magance irin wannan a gaba.