Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 13 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 13 ga Watan Nuwamba, 2019

1. An gabatar da Dokar Kalaman Kiyayya a gaban Majalisar Dattawan Najeriya a karo ta Farko

A kokarin magance matsalolin da ake samu daga wasu masu amfani da kafofin yada labarai don yada kalaman kiyayya da baci, Majalisar Dattawan Najeriya ta sake gabatar da Dokar ‘Kalamun Kiyayya’ a zauren Majalisar Dokokin kasar.

Naija News ta fahimci cewa ranar Talata da ta gabata ne karo na farko da majalisar dokoki ke kafa baki ga zanecen dokar, don kafa wata hukuma da za ta hana maganganun kalaman nuna kiyayya.

2. Hukumar DSS Sun Yi Harbe-harbe a A Lokacin da ake Zanga-zangar a saki Sowore

Ma’aikatar hukumar tsaron kasa (DSS) a ranar Talata, sun harba tiyagas don tarwatsa masu zanga-zanga da suka afka wa ofishinta don neman sakin Omoyele Sowore.

Masu zanga-zangar, a karkashin jagorancin Deji Adeyanju, sun mamaye ofishin hukumar ne a Abuja domin neman a saki Sowore nan da nan.

3. Shugabannin Jam’iyyar APC Sun Fitar da Gargadi Akan Gwamnan da ake Amfani da shi Don Tsanantawa Osinbajo

Wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke a Amurka sun yi zargin cewa akwai wata rukuni a cikin Aso Rock da ke amfani da wani Gwamna na Kudu maso Yamma, don tsananta wa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Sun kara da zargin cewa Rukunin suna amfani da gwamnan ne wajen lalata da raunana matsayin Osinbajo domin hana shi fita takarar shugabancin kasar a shekarar 2023.

4. Yahaya Bello ya Bada Hutun Aiki ga Al’ummar Jihar Kogi don Zaben Ranar Asabar

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayar da hutu ga mai’aika, ‘yan makaranta da al’umar jihar domin hidimar zaben tseren kujerar gwamna da za a yi a jihar a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba 2019.

Gwamna Yahaya Bello ya amince da ranar juma’a, 15 ga Nuwamba a matsayin ranar hutu ta jama’a da dukkanin makarantun da ke jihar.

5. Matasan Arewa sun Dage da cewa ba Shugaba Buhari ne ke Shugabancin Kasar ba

Shugaban kungiyar, Arewa Youth Consultative Forum (AYCF), Yerima Shettima ya ayyana da cewa ba Shugaba Muhammadu Buhari ba ne ke tafiyar da mulkin kasar.

Naija News ta tuno da cewa Buhari ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata cewa shi ne ke jagorancin kasar, ba kuwa shugaban Ma’aikata, Abba Kyari ba.

6. 2020: Ize-Iyamu Ya Shirya da Barin PDP zuwa APC

Tsohon mai neman kujerar gwamna a jihar Edo a shekarar 2016, Fasto Osagie Ize-Iyamu ya yi batun barin jam’iyyar sa da komawa jam’iyyarsa APC.

Naija News ta tuno cewa dan takarar gwamna a karo na biyu na Jam’iyyar PDP, Ize-Iyamu ya tsaya takarar gwamna a jihar a 2012 da 2016.

7. Sowore: An Ba mu N1m don Dakatar da Zanga-Zanga – Adeyanju

Wakilin kungiyar ‘Concerned Nigerians’, Deji Adeyanju, a ranar Talata, ya bayyana da cewa wasu masu goyon bayan gwamnati sun baiwa kungiyar kudi miliyan N1m don su dakatar da zanga-zangar adawa da suke yi kan tsare Omoyele Sowore da aka yi.

Adeyanju ya bayyana hakan ne yayin zanga-zangar da ke gudana a hedikwatar DSS da ke Aso Drive a Abuja, babban birnin kasar.

8. Zaben Kogi: Dino Melaye ya fitar da sunayen ‘Yan PDP 27 da’ Yan Sanda za su kama

Sanata Dino Melaye mai wakiltar Kogi West a majalisar dattijan Najeriya, ya yi zargin cewa rundunar ‘yan sandar Najeriya (NPF) ta na da shirin ta kama membobin kungiyar adawa ta PDP su 27 kafin zaben gwamna a Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, dan majalisar Kogi West ya yi wannan zargin ne a shafin yanar gizon a ranar Litinin, 11 ga Nuwamba.

9. Kogi: Natasha Akpoti ta tuhumi Yahaya Bello da kokarin kashe ta

A yayin da ake shirin zaben gwamna na ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Natasha Akpoti ta zargi gwamna Yahaya Bello da aiko da wasu ‘yan ta’adda domin kona gidanta a Lokoja.

Akpoti ta shigar da karar ne a ranar Litinin, inda ta ce gwamna Bello ya tura ‘yan ta’adda a harabar gidanta a yayin da take gudanar da hidimar neman zabe a Idah.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa