Connect with us

Uncategorized

Tsohon Dan Kwallon Barcelona Da Kuma Spain Ya Yi Ritaya daga Kwallon Kafa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shahararran Tsohon dan wasan kwallon kafa na Barcelona da Valencia, David Villa ya sanar da cewa ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.

Dan wasan kafar wanda ya ci Kofin Duniya a halin yanzu yana wasa ne da kulob din Vissel Kobe, da ke a Japan.

Naija News Hausa ta gane da cewa dan wasan kwallon kafan ya sanar da hakan ne a wata sanarwar da ya fitar a shafin sa na Twitter a ranar Talata, dan wasan mai shekaru 37 ya ce ya yanke shawarar ritaya daga wasan kwallon kafa ne a karshen kakar wasa ta 2019-20.

“Bayan tsawon shekaru 19 na kwarewa na a wasan kwallon kafa, na yanke shawarar yin ritaya daga buga kwallon kafar a karshen wannan kakar” inji David Villa a cikin sakon nasa.

“Na gode wa dukkanin kungiyoyin wasan kwallo, kocina da abokan karawa da suka ba ni damar cin nasara a wannan shafin. Na gode wa iyalina don tallafa mini a koyaushe.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hukumar kula da kwallon kafa ta jihar Neja ta sanar da alkawarin naira dubu N500,000 na kyauta akan kowane gwal da aka zira wa ragar ‘yan kwallon Kano Pillars a karshen gasar cin kofin Aiteo 2019.

An bayyana hakan ne a bakin Shugaban kungiyar, Hon. Adamu Aliyu, a lokacin da yake bayar da kudi na Naira Miliyan Daya da Dari Biyar (N1.5 Million) da aka baiwa ‘yan wasan kafin su kammala gasar Semi-final ga cin kofin Aiteo 2019, a hadewar su da ‘yan wasan kwallon Rivers United.