Connect with us

Uncategorized

Sarki Mai Sangaya: Jarumi, Ali Nuhu ya ce ba shi da budurwa a Kannywood

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Jarumi da Kwararre a shafin hadin fim na Hausa da aka fi sani da Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana da cewa mata guda daya kacal yake da burin mallaka a rayuwarsa.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa jarumin ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dilancin labarai ta BBC Hausa, a inda jarumin ya jaddada da cewa a bayan Maimuna matarsa, bashi da muradin kari domin ita daya ta ishe shi zaman gidan duniya.

A cikin hirar mai tsawon ‘yan mintoci hudu, jarumin da aka tambayeshi yawan yaran da yake burin ya haifa a rayuwarsa, sai ya amsa da cewa lallai yara hudu kacal yake son ya haifa, amma kuma Allah ne ya baiwa kansa sani.

Hira tayi dadi sai ga tambaya mai zafi, Am tambayi Ali iya yawan ‘yan mata da yake da shi a Kannywood, jarumin kuwa da murmushi ya amsa da bayyana cewa bashi da ‘yan mata sai dai ‘ya’ya. Ya kuwa bayyana sunayen yaran nasa a matsayin Hadiza Gabon, Maryam Yahaya da dai sauran su.

Shin wani irin shawara ne aka fi baka? Jarumin ya bayyana a fili da cewa lallai an fi bashi shawara ne kan abubuwan da suka shafi harkokin sana’arsa, da kuma dangantakarsa da mutane. A karin bayani, jarumin ya bayyana Hafiz Bello a matsayin na hannun damarsa a masana’antar duk da cewar ba kasafai ake ganinsu tare ba.

Ya kara da cewa zamaninsu ya taso ne tun yarantaka. Ya kuma bayyana cewa darakta Hafiz shine mutumin daya da basu taba samun tangarda da shi ba a Kannywood.

Kali Bidiyon Hirar Jarumi Ali Nuhu da BBC Hausa a kasa;