Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 14 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 14 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Atiku/Buhari: Kotun Koli ta Gabatar da Ranar Bayyana Dalilin Watsi da Karar PDP

Kotun kolin za ta zauna a ranar Juma’a, 15 ga Nuwamba, 2019, don yin bayanin dalilan da suka sa aka yi watsi da karar da Alhaji Atiku Abubakar ya shigar na kalubalantar sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News ta ruwaito da cewa Kotun Kolin a ranar 30 ga Oktoba, ta yi watsi da karar da Atiku da Jam’iyyar PDP suka gabatar a kan nasarar zaben Shugaba Buhari, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugaban kasa ta 2019.

2. Gwamnan Obaseki Ya Mayar da Martani akan Tsige shi da APC Tayi tare da Wasu

Gwamna Godwin Obaseki, Gwamnan jihar Edo ya yi watsi da dakatarwar da jam’iyyar Edo Peoples Movement (EPM) ta yi daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Naija News ta tuno da cewa EPM wacce shi ke rukunin jam’iyyar APC ta jihar Edo ta sanar da dakatar da Gwamna, mataimakinsa, Philip Shuaibu da Sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie, ranar Laraba da ta gabata.

3. PDP Sun Mayar da Martani kan Zancen Kisa ga Masu Yada kalaman Kiyayya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi Allah wadai da kudirin da majalisar dokoki ke gabatarwa na kudurin kisa ta hanyar rataye ga masu yada kalaman kiyayya, wadda Sanata Sabi Abdullahi ya gabatar.

Naija News ta fahimci cewa an karanta kudirin ne a karo ta farko a gaban majalisar ranar Talata da ta gabata.

4. Kogi: Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa Yahaya Bello Rancen Biliyan 10b ‘Yan Kwanaki ga Zaben Jihar Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Mista Yahaya Bello ya samu amincewar rancen nera miliyan goma din da ya nema daga gwamnatin tarayyar kasa.

Shugaban Majalisar Dattawar, Mista Ahmed Lawan a yayin magana game da rancen kudin da aka baiwa Bello, ya bayyana cewa ya zama dole a saki kudin kamar yadda Gwamnan ya nema saboda an yi jinkirta da bashi kudin da tsawon lokaci.

5. Gobara Ya Lashe Shashen Gidan Gwamnatin Jihar Neja

Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda Gobara ta kame ofishin Sakataren dindindin na gidan gwamnatin jihar Neja, sakamakon hadewar wayar wutar lantarki.

Rahoto ya bayar da cewa ya kame ne da gobara a yayin da ake kan aiki da gyara gidan gwamnatin. Gobarar ya dauki sama da mintuna 15 kafin wasu ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar suka isa wajen don tsayar da gobarar da yaduwa.

6. Gwamnonin APC Sun Bai wa Adams Oshiomhole Lokacin Da Ake Buka shin da Murabus da Matsayinsa

An baiwa Adams Oshiomhole wa’adin yin murabus a matsayin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyyar da ke mulkin Najeriya.

Naija News ta fahimta da cewa Kungiyar Gwamnonin Jiha ta Jam’iyyar APC ne suka bayar da wannan umarni ga Oshiomhole.

7. Dalilin da yasa muka Baiwa Yahaya Bello Biliyan N10bn – Lawan

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya mayar da martani kan dalilin da yasa ‘yan majalisar suka amince da N10bn ga jihar Kogi,‘ yan kwanaki kadan kafin a gudanar da zaben gwamna.

Naija News ta fahimta da cewa matakin Majalisar Dattawar ya gamu da adawa daga Sanatocin bangaren jam’iyyar PDP. Sanatocin sun kalubalanci shugaban majalisar game da lokacin da aka amince da bada rancen.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa