Connect with us

Labaran Najeriya

Bayanin Shugaba Buhari Game da Zaben Gwamnoni a Jihar Kogi da Bayelsa

Published

on

at

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa za a ba masu jefa kuri’a damar yanke hukunci a kan shugabanninsu a zaben Gwamnonin jihohin Bayelsa da Kogi.

Naija News ta rahoto da cewa Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2019 don gudanar da zaben jihar Bayelsa da ta Kogi.

A wata sanarwa da mai taimaka ma shugaban a kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya bayar, Buhari ya yi kira da a yi adalci da nuna gaskiya a yayin zabukan.

Shugaban ya kuma tuhumi hukumomin tsaro da su kasance da bin ka’ida da kuma kada su nuna banbacewa a yayin zaben a jihohin biyu.

Ya kuma bukaci al’umma masu jefa kuri’u a Bayelsa da Kogi da su yi amfani da damar su a cikin kwanciyar hankali da tsari don zaben shugabannansu.

Bayaninsa na kamar haka;

“A ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, za a bar masu jefa kuri’a a jihohi biyun, Bayelsa da Kogi don su yanke hukunci da kansu ta hanyar zabe akan wanda zai karbi ragamar shugabancin jihohinsu na shekaru hudu masu zuwa.

Na bukaci al’umma masu jefa kuri’u a Bayelsa da Kogi da su yi amfani da damar su a cikin kwanciyar hankali da tsari don zaben shugabannansu.”