Connect with us

Labaran Najeriya

Bidiyon Lokacin da El-Rufai ya Durkusa Da Rokon Mutanen Jihar Kogi Don Zaben Yahaya Bello

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Sa’o’i kafin zaben gwamna ta ranar asabar a jihar Kogi, El-Rufai ya nemi afuwa ga al’ummar jihar don yafewa gwamna Yahaya Bello wanda ke neman wa’adi na biyu a mukaminsa.

A cikin wata sabuwar bidiyo da ya riga ya mamaye layin yanar gizo, bidiyon ya nuna lokacin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya durkusa da gwiwowinsa yana rokon jama’ar jihar Kogi da su yafe wa Bello, su zabe shi a karo na biyu a matsayin Gwamna.

Naija News ta fahimci cewa wannan ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a lokacin da Jam’iyyar ‘All Progressives Congress’ (APC) ke hidimar ralin neman zabensu a Lokoja, babban Jihar Kogi.

Ka tuna da cewa El-Rufai ne Ciyaman na hidimar neman zaben Jam’iyyar APC a Jihar Kogi.

Hadi da wadanda suka halarci gangamin sun hada da Uwargidan Shugaban kasa, Dr. Aisha Buhari; matar Mataimakin Shugaban kasa, Malama Dolapo Osinbajo; da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Comrade Adams Oshiomhole.

“Mutane da yawa sun ce Yahaya Bello saurayi ne kuma ya yi fafutuka da mutane da yawa. Duk wanda gwamnan ya yi wa kuskure ko laifi, ina rokon ku da ku yafe masa duka. Matashi ne, ya kamata ya yi kuskure” Inji El-Rufai a yayin da suke hidimar neman zaben.

“Lokacin da mutum ke saurayi, ya kan yi kuskure, amma ya kamata a yi koyi daga hakan. A madadin sa, na durkusa ina rokon ku duka da ku yafe wa Yahaya Bello idan ya yi muku laifi.”

Gwamnan jihar Kaduna ya kuma lissafa nasarorin da Bello ya samar a ofis tun lokacin da aka zabe shi gwamnan Kogi.

Kalli Bidiyon Lokacin da El-Rufai ya Durkusa a kasa;