Connect with us

Labaran Najeriya

N-Power: Gwamnatin Tarayya tayi Magana Kan Dakatar da ‘yan Aikin N-Power na Farko

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin tarayyar Najeriya na tabbatar ga ‘yan aikin N-Power na tsarin farko tun shekarar 2016 da cewa tana tattaunawa da gwamnatocin jihohi da kamfanoni kan yiwuwar samar masu da ci gabada da aikin har zuwa gaba.

Gwamnati ta sanar da hakan ne da cewa ba a ba da ranar da za a tsayar da ‘yan karon N-Power na farko ba.

An sanar da hakan ne a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja, a bakin Mista Justice Bibiye, Manajan Sadarwar na Ofishin Zuba Jari na Kasa (NSIO).

Naija News ta ruwaito a baya da cewa hidimar N-Power din ta fara ne shekara ta 2016 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar, a matsayin shirin zuba jari na zamantakewar al’umma na shekaru biyu ga ‘yan Najeriya da suka kammala karatun digiri da wadanda basu yi karatun digiri ba.

Wadanda suka amfana ga hidimar kuwa zasu yi ta karbar kudi Naira Dubu Talatin (N30,000) a kowane karshin wata wasu na’urori da ya shafi aikin da aka dauke ka a tsawon lokacin da za a yi ga aikin.