Uncategorized
APC/PDP: Gwamna Jihar Bayelsa, Dickson da Matarsa Sun Jefa Kuri’arsu
0:00 / 0:00
Gwamna Seriake Dickson, Gwamnan Jihar Bayelsa da uwargidansa sun jefa kuri’un su a zaben gwamna na 2019.
Gwamnan ya isa wurin yin zaben ne tare da matar sa, Rahila a lokaci daya don aiwatar da damarsu na ‘yan kasa.
Naija News Hausa ta kula da cewa Dickson tare da matar sa halarci runfar zaben su ne ta Ward 2, PU 5, Torí-Orua community in Sagbama LGA na jihar a yayin da zaben ke gudana.
Ka tuna da cewa Gwamna Dickson na kan wa’adinsa ne na karo ta biyu a Ofishin Gwamna a Jihar Bayelsa, jiha mai cike da arzikin man fetur, zai kuma kare wa’adin ne a shekara ta 2020, a yayin da kuma yana goyon bayan Sanata Douye Diri shi ma na PDP don cin nasara ga maye gurbinsa a matsayin sabon Gwamnan Jihar.
© 2024 Naija News, a division of Polance Media Inc.