Connect with us

Uncategorized

Kogi: Bayanin Gwamna Yahaya Bello bayan da ya Jefa Kuri’ar sa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Kogi da kuma dan takaran kujerar Gwamnan Jihar a karo ta biyu a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yahaya Bello ya jefa kuri’un sa a mazabar ta sa.

Kamar yadda rahoton Naija News ta ruwaito ‘yan sa’o’i da suka wuce da cewa Gwamna Bello ya isa mazabarsa da kuma jefa kuri’un sa da misalin karfe 8:45 na safiyar ranar Asabar tare da matar sa Hajia Amina Bello a unguwar Agasa 1.

Da yake zartawa da manema labarai jim kadan bayan da ya jefa kuri’ar, Gwamna Bello ya kasance cike da yabo saboda kwarewar hukumar gudanar hidimar zaben (INEC).

Ya yaba wa INEC saboda tabbatar da cewa na’urar karanta katunan zaben suna aiki kamar yadda ya kamata sabanin lokacin zaben shugaban kasa da ya gabata, inda ya lura da cewa wasu katunan karanta katin zaben basu yi aiki ba.

Bello a cikin hirar da yake magana game da yiwuwar sakamakon zaben, Gwamnan ya nuna gamsuwar cewa za a ci gaba da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma jadada da cewa yana da tabbacin cewa Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) tabbas za ta lashe zaben Gwamnonin ta yau, Asabar da kuma zaben gidan Majalisar Dattawa a Jihar.