Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Asabar, 16 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Asabar, 16 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Komo Najeriya Bayan Ziyarar Kai Tsaye Zuwa Kasar Ingila

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar juma’a da yamma ya dawo kasar Najeriya bayan wata ziyarar sirri da ya kai a kasar Burtaniya.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ruwaito a baya da rahoton cewa ana dubin dawowar Shugaba Buhari a kasar ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, kamar yadda shugaban ya sanar ta bakin maitaimaka masa wajen yada labarai a layin yanar gizo, Garba Shehu.

 

2. Kogi: Ina da Shaidar Da Ya Nuna Cewa Gov Yahaya Bello Zaiyi Makirci A Zaben Asabar – Dino

Dan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP da kuma dan takarar kujerar Sanata a ‘Kogi West Senatorial’ a zaben na ranar Asabar, Dino Melaye, ya yi ikirarin cewa an riga an sanya tsare-tsare domin kadamar da makirci a zaben da za a gudanar a gobe, Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Dino ya jadada da cewa lallai akwai shirin don sayar da zaben gobe ga gwamnan jihar, Yahaya Bello da kuma Smart Adeyemi, dan takaran gidan Majalisa.

3. ‘Yan Garkuwa Sun Hari Gwamna Makinde a Wata Otal da ke a Lokoja

Wasu Mahara da Makami a ranar juma’a da ta wuce sun kaiwa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde hari a wani otal a Lokoja, jihar Kogi inda gwamnan ke hutawa.

Rahoto ya bayyana da cewa ‘yan garkuwan sun hari Otal din da Gwamna Makinde da wasu shugabannin PDP suka kwana ne a misalin karfe 12.50 na yamma.

4. Bayelsa: Kotun daukaka kara ta umarci INEC da Kada ta tsayar da dan takarar APC, David Lyon, daga Tseren Zaben Jihar

Kotun daukaka kara wacce ke zaune a Fatakwal ta umarci Hukumar gudanar da zaben kasa da cewa kada ta dakatar da dukkanin zabukan fidda gwani da dan takarar gwamna, David Lyon ke a ciki.

Naija News ta kula da cewa hakan kuma zai baiwa APC da dan takararta daman takara a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Bayelsa.

5. DSS Sun Ba da Dalilai Da ya Sa Basu Saki Dasuki, EL-Zakzaky da Sowore ba

Ma’aikatar Tsaron Jiha-da-Jiha (DSS) ta yi bayanin kan dalilin ci gaba da tsare Kanal Sambo Dasuki (rtd.), Sheik Ibrahim El-Zakzaky da Omoyele Sowore.

Ka tuna da cewa ‘yan Najeriya sun yi Allah wadai da mataki da manufar ‘yan sanda na kin bin umarnin kotu da kuma kiyaye shawarar wasu masu ruwa da tsaki a kasar kan tsare mutane Ukun.

6. WAEC ta Saki Sakamakon jarrabawar watan Nuwamba da Disamba

Ma’aikatar Jarabawan WAEC ta saki sakamakon jarrabawar dalibai da suka zauna a jarrabawar kammala Makarantar Sakandare ta shekarar 2019 a Najeriya.

An sanar da hakan ne a bakin Mista Olu Adenipekun, shugaban ofishin WAEC ta kasar Najeriya a wata taron manema labarai a jihar Legas.

7. Kotun Koli ta Ba da Dalilin Yin Watsi da Karar Atiku Ga Buhari

Kotun Koli a ranar Juma’a da ta wuce ta tabbatar da hukuncin Kotun daukaka karar Shugaban kasa wacce ta dage da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci ya samu damar yin takara a zaben shugaban kasa na 2019.

Naija News ta ba da rahoton cewa Kotun Kolin a ranar 30 ga Oktoba, tayi watsi da karar da Atiku da Jam’iyyar PDP suka gabatar a kan nasarar zaben Shugaba Buhari, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

8. Goodluck Jonathan yayi Magana kan zaben gwamna a Bayelsa da Kogi

Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana damuwarsa gabanin zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa da aka shirya ranar Asabar.

Tsohon Shugaban wanda ya koka da yawan rikice-rikice da rahotannin tashin hankali da ya riga ya gudana tun kafin zaben, ya yi kira da a kame kuma a kwantar da hankulan dukkan masu ruwa da tsaki.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa