Connect with us

Uncategorized

Kalli Dukan Sakamakon Zaben Jihar Bayelsa da INEC ta Sanar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasa, INEC ta gabatar da sakamakon zaben Bayelsa na karshe daga dukkan kananan hukumomin (LGAs) inda aka gudanar da zaben gwamnonin.

Naija News ta ruwaito tun da farko cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ayyana David Lyon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyyar da ke mulkin Najeriya, a matsayin wanda ya yi nasara a zaben Gwamnonin Bayelsa.

Rahoton ya bayyana Lyon da samun yawar kuri’u 352,552 da ya kaishi ga kayar da abokan karawarsa da kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, Duoye Diri, wanda ya sami yawar kuri’u 143,172.

Wannan sakamakon zaben da rahoton nasarar David Lyon ya tabbatar da jihar Bayelsa a zaman jihar APC, musanman sake lashe zaben Jihar a wannan karo kuma.

Ga Sakamakon Zabunan a kasa daga Kananan Hukumomin Jihar;

S/N LGA APC PDP

1

BRASS 23,831 10,410

2

EKEREMOR 21,489 18,344

3

KOLOKUMA/OPOKUMA 8,934 15,360

4

NEMBE 83,041 874
5 OGBIA 58,016 13,763
6 SAGBAMA 7,831 60,339

7

SOUTHERN IJAW 124,803 4,898

8

YENAGOA 24,607 19,184
TOTAL 352,552 143,172