Uncategorized
Kogi: Ban Amince da Sakamakon Zabe ba – Musa Wada ya Kalubalanci Hukumar INEC
Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.
Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.
Naija News ta fahimci cewa a cikin sakamakon zaben da aka riga aka sanar, gwamna Bello na gaban sauran ‘yan takara da yawar kuri’u.
Rahoton sakamakon ya nuna da cewa Gwamna Bello yana kan gaban sauran ‘yan takara 23 da yawar ƙuri’u sama da dubu 200, 000 a cikin kananan hukumoi 15 daga kananan hukumomi 21 da ke a Jihar, kamar yadda aka sanar.
Wada wanda ya yi magana da manema labarai a Lokoja a ranar Lahadi, ya yi watsi da sakamakon, yana zargin cewa mataimakin gwamnan jihar, Cif Edward Onoja tare da hukumomin tsaro suna tafiya ba tare da izini ba kuma suna ziyartar cibiyoyin tattara kuri’u inda suke sauya sakamakon don fifita jam’iyyarsu.
“Lallai PDP zata kalubalancin wannan sakamakon a kotu.” inji Wada.
“Sakamakon ba tabbacin gaskiyar abin da ya faru ba ne a runfar zabe. Mutanen jihar sun zabi PDP amma APC ta canza sakamakon da ya gamshe su.
Sakamakon da hukumar INEC ta bayyana har zuwa yanzu sakamakon ba zamu yarda da hakan ba. An riga an canza duk sakamakon da aka samu a kowace runfar zabe kuma za mu kalubalanci wannan zaben. Ba gaskiyar abinda ya gudana aka sanar ba.” inji shi.
“Ni ne dan takarar Jam’iyyar PDP kuma ba lallai ne in jira har sai sun kashe ni ba. Dole ne in yi kira ga jama’ar Najeriya su sani cewa APC ta yi magudi a zaben,” in ji Wada.