Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 18 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 18 ga Watan Nuwamba, 2019

1. INEC ta Dakatar Da Sanar da Sakamakon Zaben Gwamnonin Kogi

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Lahadi ta sanar da cewa ta dakatar da sanarwar sakamakon zaben gwamnoni na ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi.

Wannan sanarwan an bayar da ita ne a bakin Babban Ofisan da Shugaban Hukumar INEC ta Jihar, wanda ke jagorancin hidimar zaben.

2. Tsoracewa A Yayin da INEC ta Fara Bayyana Sakamakon zaben Bayelsa

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka gudanar ranar Asabar.

Naija News ta fahimci cewa an jinkirta ne da sanar da sakamakon wanda ada aka shirya da farawa a karfe 10 na safiyar ranar Lahadi a cibiyar Farfesa Mahmood Yakubu.

3. Fayose ya Kalubalanci zaben Jihar Kogi da Bayelsa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya koka da sakamakon zaben gwamnonin jihar Kogi da na jihar Bayelsa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa duka zabukan da suka gudana a ranar Asabar sun kasance da rikice-rikice da kuma magudi.

4. Dalilin da yasa Membobin Edo na APC ke son Obaseki ya fita – Airhavbere

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo, Charles Airhavbere, ya ba da dalilan da suka sa membobin jam’iyyar ke son tsige Gwamna Godwin Obaseki.

A yayin da yake zartawa da manema labaran NAN a ranar Lahadi, tsohon mai neman takarar gwamna a Edo ya zargi Godwin Obaseki da kin sauraren muryar dalilai.

5. Abinda aka ga Yahaya Bello na yi yayin da INEC ke sanar da sakamakon zaben Kogi

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka hango Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a hotuna tare da mukarraban sa a Lokoja, babban birnin jihar, yayin da suke shan shayi da nishadewa.

Ka tuna kamar yadda Naija News ta sanar, ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba ne Hukumar Zabe ta gudanar da zaben Gwamnonin jihar Kogi.

6.  Ban Amince da Sakamakon Zabe ba – Musa Wada ya Kalubalanci Hukumar INEC

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.

Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.

7. Zaben Kogi: INEC ta ayyana ma’aikata 30 da suka Bata

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC), ta bayyana jami’anta 30 da suka bace a zaben gwamnoni da aka yi a Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta fahimta da cewa mutane 30 din da suka bata suna cikin malaman zabe da aka dauka don hidimar zaben zaben gwamnoni na ranar Asabar a jihar Kogi, arewa maso-tsakiyar Najeriya.

8. Kotun daukaka kara ta Soke Dan Jam’iyyar PDP a Majalisa

Kotun daukaka kara da ke zaune a Owerri ta tsige dan majalisa mai wakiltar mazabar Isiala Mbano / Onuimo / Okigwe da ke jihar Imo a majalisar wakilai, Obinna Onwubuariri.

Da yake yanke hukuncin a ranar Asabar, shugaban kwamitin, Mai shari’a R.N Pemu, ya bayyana da cewa nasarar Onwubuariri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a watan Fabrairu ya kasance ne da sabawa dokar zaben kasa kamar yadda aka ayyana tun shekarar 2010.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa