Connect with us

Labaran Najeriya

Da A Ce Annabi Isah zai kasance anan, Da zai Kalubalanci Yanayin Najeriya – Obasanjo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, yayin da yake magana kan halin da Najeriya ke ciki, ya bayyana cewa idan har Annabi Isa zai kasance a wannan kasar a wannan lokacin, zai yi korafi kan yadda masu iko ke tafiyar da mulkin kasar.

Tsohon Shugaban a cikin sanarwar sa ya karfafa malaman adinin Kirista da cewa kada su yi shuru game da abin da ke faruwa a kasar amma a koyaushe su fadi gaskiya ga mutanen da ke kan mulki.

Obasanjo ya bukaci kirista da su yi koyi da irin rayuwar Yesu kuma su yi wa’azin hadin kai a tsakanin su, ya kara da cewa rashin yin hakan na iya sanya su a hannun abokan gaba da makiya.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron shekara da shekara ta karo na 64 na cocin Foursquare Gospel Church da aka yi a harabar cocin a kan Shiyar Lagos-Ibadan Expressway, Ajebo, Jihar Ogun.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kungiyar Makiyaya da aka fi sani da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta gargadi shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya da kama tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo akan zargin da yake da makiyaya Fulani.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa kungiyar sun bayyana hakan ne a yayin da suke mayar da martani game da wata wasika da Obasanjo ya wallafa ga shugaba Muhammadu Buhari ranar Litini, 15 ga watan Yuli da ta gabata, akan yanayin matsalar rashin tsaro ke ake fuskanta a kasar Najeriya.