Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 19 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 19 ga Watan Nuwamba, 2019
1. INEC ta ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan Kogi
Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Litinin, ta bayyana sakamakon karshe da kuma wanda ya yi nasara a zaben gwamna na Kogi na shekarar 2019.
Jami’in hukumar INEC da ya jagoranci hidimar zaben gwamnan da ta majalisa, Farfesa Ibrahim Umar Garba, ya bayyana sakamakon, a ranar Litinin, 18 ga Nuwamba a cibiyar tattara kuri’u da ke a Lokoja, babban birnin jihar bayan an samu sakamako daga dukkan kananan hukumomin.
2. Isah Almasihu zai Kalubalanci Yanayin Najeriya Idan Da A Ce Zai Kasance anan – Obasanjo
Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, yayin da yake magana kan halin da Najeriya ke ciki, ya bayyana cewa idan har Annabi Isa zai kasance a wannan kasar a wannan lokacin, zai yi korafi kan yadda masu iko ke tafiyar da mulkin kasar.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron shekara da shekara ta karo na 64 na cocin Foursquare Gospel Church da aka yi a harabar cocin a kan Shiyar Lagos-Ibadan Expressway, Ajebo, Jihar Ogun.
3. Abin da Jonathan ya ce Bayan INEC ta ayyana Lyon da lashe zaben Gwamna a Bayelsa
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya taya dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Lyon murnar nasarar lashe zaben jihar Bayelsa.
Naija News ta rahoto cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ayyana David Lyon a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnonin Bayelsa wanda aka yi Asabar, 16 ga Nuwamba 2019.
4. Wada ya Mayar da Martani Bayan da INEC ta Gabatar da sanarwar lashe zaben Kogi ga APC
Dan takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Musa Wada, ya nuna rashin gamsuwarsa da sanarwan Hukumar Zaben Kasa (INEC) saboda yadda aka gudanar da zaben na Jihar Kogi.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a ranar Litinin, ta ayyana sakamakon karshe da kuma sanar wanda ya yi nasara a zaben gwamna na Kogi na 2019.
5. Gobarar Motar Tanki Ya Tafi da Rayuka 5 a Jihar Kogi
Rahoton da ke isa ga Naija News daga manema labarai ya bayyana da cewa a kalla mutane biyar suka mutu, wasu kuma da raunuka yayin da motar tankin da ke dauke da man fetur rutsa da wasu motoci cikin Kogi.
A haka wannan al’amarin ya sanya mutanen Felele da ke a karamar Hukumar Lokoja cikin zaman makoki da jinya bayan a kalla mutane biyar ne aka ruwaito sun mutu sakamakon hatsarin da ya afku da motar tankin.
6. Shugaba Buhari Yayi Taron Siri da Oshiomhole, Gwamnonin APC da Sauransu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta wuce ya gana da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, a fadar shugaban kasa, Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa an gudanar da taron ne da kofa kulle.
7. Dubi Dalilin da yasa Timi Frank ya nemi Uche Secondus Da Neman Afuwa ko Yayi Murabus
Tsohon Mataimakin Kakakin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Timi Frank, ya yi kira ga Shugaban neman zabe ga Jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da Kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar da su nemi afuwa ko su yi murabus da matsayinsu sakamakon asarar Jam’iyyar a zaben Jihar Bayelsa a watan Nuwamba 16.
Frank ya bayyana hakan ne yayin da yake taya murna ga zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon.
8. An Kame Tsohon Ofisan Janara, Adoke a Dubai
Kungiyar ‘yan sanda ta kasa da kasa ta kama tsohon babban Ofisan Tarayya da kuma ministan shari’a ga Najeriya, Mista Mohammed Bello Adoke (SAN) a Dubai.
Naija News ta fahimci cewa hakan ya faru ne da babban Lauyan, wanda a isarsa Dubai a ranar Litinin, 11 ga Nuwamba, don shirin duba lafiyar jikinsa aka kame shi, sannan aka tsare shi.
9. Amurka, Burtaniya, Tarayyar Turai sun yi Allah Wadai da Hukuncin zaben Bayelsa da Kogi
Kasar Amurka, Burtaniya da Tarayyar Turai (EU) sun yi Allah wadai da mummunan tashe-tashen hankula da aka samu yayin zabukan gwamnonin Bayelsa da Kogi.
Naija News ta tunar da cewa Hukumar Zaben Kasa (INEC) ce ta gudanar da zaben gwamnonin Bayelsa da Kogi a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba da ta gabata.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa