Connect with us

Uncategorized

Wata Budurwa ta yi yunkurin rungumar Taransufoma bayan anyi mata auren dole da Tsoho

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bisa rahoton da ke isa ga Naija News Hausa a wannan lokacin, wata al’amari ta faru a ranar Juma’a, 15 ga wannan Nuwamba 2019 da ta gabata, Inda wata ‘yar yarinya ta yi yunkurin shiga cikin na’urar da ke bada hasken wutar lantarki, watau taransufoma.

Abin bisa wata majiya ya faru ne a unguwar Sharada da ke yankin karamar hukumar birnin Kano bayan da ta yo tattaki tun daga unguwar Rimin Kebe da ke yankin karamar hukumar Ungogo. Ta bayyana ga daya daga cikin wadanda suka yi daukin ta da koke-koken cewa lallai an yi mata auren dole ne da wani tsoho da bata so. A don haka ne take neman mafita.

Bisa bayanin mazaunan yankin, matashiyar da ba a bayyana sunanta ba, a bayan da ta gama koke-koken ta da su sai ta nufi dakin da na’urar bada wutar lantarkin ke ciki don kawo karshen rayuwarta.

Godiya ga Allah, sakamakon gaggawar da aka yi bata cin ma yin hakan ba tukuna har aka rike ta. A ganin wannan yunkurin ne yasa kungiyar kare hakkin dan Adam ta shiga lamarin. Shugaban kungiyar, Karibu Lawan Kabara, ya bayyana cewa zasu yi iyakar bakin kokarinsu wajen ganin sun kwato wa matashiyar hakkinta daga iyayen.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wata yarinya ‘yar shekara goma sha bakwai (17) da haihuwa mai zama a yankin Albarkawa a cikin garin Gusau ta jihar Zamfara, mai suna Aisha, ta haska wa kanta wuta sakamakon cewa Saurayinta ya kasa ga iya biyan sadakin aurenta saboda rashin kudi.

Bisa bayani da Maƙwabcin A’isha ya shaida wa Aminiya, ya bayyana da cewa ta yanke hukuncin kashe kanta ne bayan da ta samu labarin cewa saurayin da ke neman ta da aure ya kasa iya biyan kudin sadakin da iyayenta suka yanka masa domin shirya bikin aurensu.