Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Bindiga Sun Kashe A Kalla Mutane 18 a Jihar Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘yan hari da makami a daren ranar Lahadi sun kashe a kalla mutane 18 a cikin garin Karaye cikin karamar hukumar Gummi na jihar Zamfara, bisa bayanin mazauna da jami’an gwamnati.

Mazauna yankin sun fada da cewa wannan harin shi ne mafi muni a cikin ‘yan watannin da suka gabata a yankin, a yadda suka ga ‘yan hari da bindigar sun hari unguwar ba tare da fuskantar kalubale daga jami’an tsaro ba. Sun bayyana da cewa mutane da dama sun samu raunuka da dama a lamarin.

Wata majiya da manema labaran PREMIUM TIMES suka gane da tabbatar, ya nuna da cewa mutane 18 ne suka mutu a harin da ya faru a missalin karfe 5.30 na maraicen ranar Lahadin.

Majiyar  ta bayyana da cewa harin mayar da martani ne ga kashin ‘yan ta’adda kusan bakwai da ‘yan banga suka yi a yankin tun a ranar 3 ga watan Nuwamba, bayan da aka bayyana ‘yan ta’addan da rigaya da tuba.

Ko da shike dai, wata majiya kuma a Asibitin Tarayyar yankin a ranar Litini ta bayyana da gano gawaki 20 a dakin ajiye gawaki bayan da abin ya faru.

Mataimakin musamman ga gwamna Bello Matawalle kan lamurran tsaro, Abubakar Dauran, ya kuma bayyana da cewa wannan harin ramuwar gayya ce daga wasu Fulani wadanda aka kashe danginsu a harin farko da suka kai kan wata kasuwa da ke unguwar Bardoki da ke Gummi makonni biyu da suka gabata.

Mista Dauran ya ce wani rahoto da ya ke dauke da ita ta bayyana da cewa mutane 10 ne suka mutu a harin. Ya yin Allah wadai da harin ya cewa ya kamata a zargi wata kungiya da ake kira “Yansakai, wanda ya ce ya sun kashe Fulani da yawa a harin farko da aka yi”.

Ya kara jadadda da cewa an riga an kame a kalla mazauna bakwai, ‘yan kungiyar ‘Yansakai, da kuma wasu cewa an kashe hadi da wasu tsohi a harin.

“An dakatar da masu aikin banga a cikin jihar, amma har yanzu suna ci gaba da ayyukansu, suna dakile kokarin samar da zaman lafiya da gwamnatin ke kokarin yi. Tsarin zaman lafiyar kuwa zai tabbata” inji shi.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da cewa kada su karaya sakamakon harin, yana mai cewa gwamnati tana kan gaba da magance irin wannan mumunar halin.