Uncategorized
Yaron Shehu na Borno, Kashim Ya Nakasa Jami’in Civil Defence da Mota
A wata rahoto da aka bayar ta hannun manema labaran PRNigeria, an bayyana wani abin tashin hankali game da zargin dan Shehu na Borno, Kashim Abubakar- Elkanemi, wanda ya nakasar da wani jami’in Tsaro na Rundunar Civil Defence (NSCDC) yayin tseren mota a cikin Maiduguri, jihar Borno.
Naija News ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Nuwamba, da misalin karfe 5:30 na yamma a Ramat Square Maiduguri, lokacin da wata kungiyar yaran wasu manya da fitattun mutane a jihar Borno da aka fi sani da kungiyar ‘Yarwa Squad’ suka hau kan titi da tseren motoci masu tsadar gaske.
Jami’in da aka yi wa raunuka, Mista Usman Bakari, shi ne Babban Jami’in NSCDC wanda ke kula da yakunan Maiduguri.
A cewar wani da yayi shaidar gani lamarin, koda shike an hana bayyana sunansa, amma ya tabbatar yadda abin ya faru ga manema labarai a ranar Litinin, da cewa dan Shehu ne ya raunata jami’in bayan da ya nemesu da dakatar da tseren don hana faruwar hadari.
Mai shaidar yaci gaba da bayyana da cewa wasu daga cikin matasan sun korawa jami’in NSCDC din wuta da cewa ya zai hana Dan Shehu yin duk abinda yake so.
“Wannan kasar mahaifinsa ne kuma zai iya duk abinda ya gardama, inji amshin su.”
“Ana cikin hakan ne motoci biyu suka yi yunkurin yiwa jami’in rauni a kokarin su buge shi, amma jami’in ya samu tserewa, amma dan Shehu ya sake juyowa da nasa motar yayin da yake cikin gudu sai ya rutsa da jami’in tsaron a yayin da sauran jami’an suka tsira da bugun motar da kyar. anan take kuwa suka watse da motocin su bayan nakasa jami’in.”
Ya kara da cewa an bar jami’in ne a cikin ramin jini tare da raunuka a yayin da aka kai shi Asibitin kwararru na Maiduguri domin yi masa magani.
Ko da shike Hukumar NSCDC ta Borno ta ce ta kama wani da ake zargi da hada hannu a lamarin yayin da dan Elkanemi ya tsere.