Connect with us

Uncategorized

Ba na Tsoron Mutuwa – inji Tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana da cewa daya daga cikin manyan damuwa da kudurinsa a rayuwa shi ne, samar da shugabanni na kwarai ga Afirka.

Tsohon shugaban wanda ya yi takaicin cewa duniyar ba ta da shugabanni na kwarai, ya yi kira ga matasa da su tashi, su farfadar da kasar Najeriya, su kuma karfafar da Afirka gaba daya.

Obasanjo ya fadi hakan ne yayin da yake magana a ranar Talata a wani taron tattaunawa na kwana biyu na Shugabancin Matasa na Shugaban Kasa, wanda aka gudanar a Cibiyar Raya Matasa ta Olusegun Obasanjo, Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Cif Obasanjo ya bayyana da cewa a wannan lokacin da riga ya tsufa, bai jin tsoron ya mutu.

Ya kuwa nuna godiyarsa ga Allah kan damar da ya ba shi na shugabancin kasar a mulkin soja da kuma a matsayinsa na shugaban kasar a dimokiradiyya.

Obasanjo ya lura da cewa akwai bukatar matasa a duk yankin Afirka don samun jagoranci kwarewa daga shugabannin da suka gabata.

“Ba na tsoron mutuwa a shekaruna, Allah ya yi min falala kuma ina godiya da albarkar da Allah ya yi mini a cikin wadannan shekarun.”

“Damuwana na tsawon shekaru da yawa shine gina shugabannin Afirka. Babban damuwana shi duban gobe, goben kuma ta fara a yau” inji Obasanjo.