Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Zamfara, Matawalle ya Dakatar da wani Babban Wakili a Jihar

Published

on

at

advertisement

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya amince da dakatar da wani Babban Shugaban Gummi, Alhaji Abubakar Bala Gummi, (Bunun Gummi).

An bayyana a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun Sakataren dindindin na Jihar, Ministan Hukuma da Ayyukan Al’umma, da cewa an dakatar da Alhaji Aliyu Bello Maradun, wakilin gundumar akan wata zargin da aka yi masa na tallafa wa ‘yan garkuwa a jihar.

Sanarwar na cewa; 

“An dakatar da Alhaji Abubakar Bala Gummi daga matsayinsa a gagauce har sai an kamala bincike da ake akansa kan wasu kashe-kashe da ya gudana a yankin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutanen da basu da wata laifi” Inji Shi.

Kodashike, A halin da ake ciki gwamna Bello Mohammed Matawalle ya riga ya kafa kwamiti da zata binciki musabbabin kisan mutane da aka yi a kwanan nan a kauyen Karaye wanda a cewarsa abin takaici ne.

Yayi la’akari da yunƙurin zaman lafiya da gwamnatinsa ta gabatar wanda ya kawo kwanciyar hankali a tsakanin watanni huɗu a da suka gabata a wa’addinsa.

Gwamnan ya yi alwashin cewa zai tabbatar da cewa an hukunta kowane mutum ko wata kungiya da ta yi kokarin dakile tsare tsaren da gwamnatin sa ke yi.