Uncategorized
Abin Takaici: Kalli Hotunan Lallatacen Gidan Kwancin Dalibai Mata a Jihar Neja
0:00 / 0:00
Naija News Hausa ta ci karo da Hotunan mummunan lalacewar Kwalejin Ilimin ta Mata na Gwamnati da ke a Agaie a jihar Neja.
Hotunan da a haka ya riga ya mamaye layin yanar gizo da barin ‘yan Najeriya a mamakin yadda aka bar makarantar, musanman dakin kwanan daliban da lalacewa da muni hakan.
Yawancin ‘yan Najeriya na zargi da mamakin yadda gwamnati da masu kula gudanarwar kwalejin ke tsammanin ɗalibai su iya gane abinda ake koyardasu a cikin wannan yanayin.
Idan ka dubi hotunan da kyau, ka ga yadda gidan kwanan dalibai ‘yan matan ya lalace da zubar ruwa. Rufin tuni ya fara rushewa a ciki.
Ga shi a fili sai ma ‘yan matan su tattara bokitansu don taron ruwan sama da ke zubowa daga sararin sama a lokacin damana.
Kalli Hotunan a Kasa;
© 2024 Naija News, a division of Polance Media Inc.