Connect with us

Uncategorized

Labaran Kwallo: Babban Koci, Mourinho ya Koma Kulob din Tottenham

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mourinho ya bar Tsohon Kulob din sa da Komawa Tottenham

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta Ingila ta tabbatar da nadin Jose Mourinho a matsayin sabon manajanta.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Mourinho ya rattaba hannu kan yarjejeniyar har zuwa karshen gasar kwallon kafa ta shekarar 2022/23 tare da Spurs, kuma zai jagoranci kungiyar a wasan Premier League da West Ham a ranar Asabar.

Wata sanarwa da kungiyar kulob din ta bayar ta ce: “Muna matukar farin cikin sanar da nadin Jose Mourinho a matsayin Kocin kungiyar kan kwantiragin da zai kare har zuwa karshen shekara ta 2022/23.”

“Jose yana daya daga cikin manyan manajojin duniya da ya taba da lashe kofuna 25. Ya shahara da kwazonsa kuma ya jagoranci FC Porto, Inter Milan, Chelsea, Real Madrid da Manchester United a yawon sa wajen Koci.

A yayin mayar da martani ga sabon ci gaban, Mourinho fada da cewa “Na yi farin cikin kasancewa tare da kungiyar da ke da manyan gadajeni da kuma irin wadannan masu goyon baya. Inganci a cikin rukunin ‘yan wasan da kuma makarantar hodar da sabbi da kananan ‘yan kwallo ya faranta min rai. Yin aiki tare da wadannan ‘yan wasan abu ne wanda ya ja mini hankali kwarai da gaskei.”

Wannan matakin komawar Mourinho a Tottenham ya zama da tabbaci ne bayan da kulob din a daren ranar Talata da ta wuce ta sanar da korar tsohon kocin kungiyar, Mauricio Pochettino.

KARANTA WANNAN KUMA; Wata Budurwa ta yi yunkurin rungumar Taransufoma bayan anyi mata auren dole da Tsoho mai shekaru 70.