Connect with us

Uncategorized

Takaitaccen Bayanin Rayuwar Ali Jita

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wannan Itace Taikatacen Labarin Shahararran Mawaki, Ali Jita

Ali Jita shahararran mawaki ne mai zamaninsa a Kano, sananne ne kuwa a wake-wake a fagen shirin finafinan Hausa, kuma ya shahara kwarai da gaske a yawancin finafinan hausa.

Ainihin sunan sa itace Ali Isa Jibril, kuma an haife shi ne a unguwar gyadi-gyadi a cikin badalar Kano dake a Arewacin Najeriya.

Makarantar da Ali Jita Ya Je:

Ali yayi karatun farkon sa na Firamare ne a wata makarantar da Sakandare duk a birnin Legas, a wata makarantar sojojia, kamin dada ya bar Legas zuwa brinin Tarayyar kasa, Abuja.

Mawakin ya koma jihar Kano ne bayan karatun Sakandare inda ya kammala karatun sa na Difloma akan harkar mulki da kuma a fannin na’ura mai kwakwalwa, hade da wani difloma a shafin Computer, a wata makarantar Intersystem ICT School, duk anan Kano.

Ali jita da Matarsa

Lokacin da Ali Jita Ya Fara Wake-Wake:

Shahararren, Ali Jita bisa bincike ya tsunduma a harkar wake-waken Hausa ne a tun daga shekarar 2009 a inda kuma nan da nan ya samu karbuwa a zukatan masoya da al’umma sakamakon kwarewar sa da kuma zazzakar muryar da Allah ya bashi.

Mawakin sanadiyar kwarewarshi a yanzu haka ya samu nasarori da dama inda ya lashe kyaututtuka masu tarin yawa sannan kuma ya fitar da kundin wakoki da yawa.

Wakokin Ali Jita:

Mamana, Arewa Angel, Gimbiyar Mata, Arewa, Kyece, Yara Yara, Masoyiyata Indo, Indo, Nanaye, Allah Sarkin Duniya, Farar Diya, Tarkon, Qauna, Ladidiya, Giyar Mulki, Sona Sinadari, Halimatu Sadiya, Love, Duniya, Rayuwa, Buri Uku, Fadakarwa, Mata, Watan Azumi, Zamana Aure, Rabbana, Zakka, Jawabi, Muyi Shilo da dai sauransu…

Ga sabuwar Waka Da Ali Jita ya fitar; Arewa Angel

Iyalin Ali (Watau Mata Da Yara):

Bisa bincke, Naija News Hausa ta fahimci cewa Ali Jita nada mata daya ne kawai, Allah kuma ya albarkace su da samun ‘ya’ya biyu.

Ali dai masoyin wasan kwallon kafa ne, kuma shi babban masoyin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ne.

Ali Jita ya yi fita a shirin Fina-finai kamar su Gimbiya Bakandamiya, Kishi, Murmushin Alkawari Zaman Aure, da kuma Garin Gimba.