Connect with us

Uncategorized

Abin da Ya Dace ‘Yan Sanda Suyi da Wadanda suka Kashe Shugaban Matan PDP a Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takarar kujerar Gwamna a zaben Jihar Kogi, karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Musa Wada ya yi kira ga ‘yan sandan Najeriya da su tabbatar da kamo wadanda suka kashe Acheju Abu.

Ka tuna cewa a yayin wata arangama ta jini da magoya bayan jam’iyyu suka yi ranar Litinin a Ochadamu, karamar hukumar Ofu na jihar Kogi, ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Willam Aya, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Talata, ya ce wata tsohon Kansila a karamar hukumar, Malama Salome Abu da Mista Awalu Zekeri sun mutu a rikicin.

Ofisan ya kara da cewa rikicin ya fara ne sakamakon rashin fahimta da ya afku tsakanin Zekeri na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Mista Goodwin Simeon, memba a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

“Don yin ramuwar gayya, wasu matasa da suka fusata a cikin Ochadamu sun tafi gidan Mista Simeon Abuh, wanda yana zaman kawu ne ga wanda ake zargin kuma suka haska wa gidan wuta. ‘Yar shekara 60, Malama Salome Abuh ta mutu ne a cikin gidan sanadiyar ƙone ta har lahira” inji Aye.

Dan takaran, Wada a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin a ranar Talata ya yi kira ga ‘yan sanda Najeriya su bincika tare da kama wadanda suka kashe Abu.

KARANTA WANNAN KUMA: Yaron Shehu na Borno, Kashim Ya Nakasa Jami’in Civil Defence da Mota