Uncategorized
Ahmed Musa, Kyaftin din Super Eagles Ya Dauki Nauyin Biyan Kudin ‘Yan Makaranta 100
Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya tabbatar da aniyarsa na tallafawa daliban Najeriya 100 ga jami’ar Skyline wacce ke a cikin jihar Kano.
Naija News Hausa ta fahimta cewa Tsohon dan wasan kwallon kafa na Leicester City Musa ya shafe shekaru da yawa a Kano yayin da yake girma sannan kuma ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a gasar firimiya ta Najeriya kafin ya koma Turai.
A ranar Laraba, 20 ga Nuwamba da ta wuce Ahmed Musa ya kasance a jami’ar Skyline da ke a Kano, inda aka ba da sanarwar sa a matsayin jakadan makarantar. Dan shekaru 27 da haihuwan zai taimaka wajen bunkasa harkar ilimi har ma da wasu ayyukan yau da kullun kamar su wasanni da koyar da jagoranci.
Kalli sakon da aka wallafa a shafin Twitter mai bada tabbacin lamarin;
https://twitter.com/Usainbalakanam/status/1197229018686394370
Ga lokacin da Ahmed Musa ya Rattaba Hannu ga Takardan Gudumuwar;
Musa ya ce; “Ni babban mai imani ne game da mahimmancin ilimi saboda haka, farin cikina da shiga cikin wannan babbar kungiyar don inganta wannan hangen nesa na zama duk abin da kuke so ku kasance a rayuwa muddin zaku yi hange da kudurin haka.”
“Don haka, ina farin cikin sanar da ku cewa zan tallafa wa ɗalibai 100 a wannan jami’a. Haka ne! 100” Inji Shahararren Dan Kwallon.