Connect with us

Uncategorized

Jihar Kano: Kotu Ta Soke Nadin Masarauta Hudu da Ganduje Ya Kafa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Alhamis, 21 ga Watan Nuwamba 2019 ne wata babbar kotun jihar Kano ta soke nadi da kirkirar wasu masarauta guda hudu a jihar Kano.

Ku tuna Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano, ya mika Alkibba da Sandar Shugabanci ga sabbin Sarakai hudu da ya nada a Jihar.

A yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Usman Na’abba, alkalin kotun, ya ce kirkirar masarautun hudu ba bisa tsari da suka dace ba ne, in ji rahoton gidan talabijin na Channels.

Wannan gidan labarai ta tuna da cewa ƙirƙirar ƙarin masarautuka ya jawo cece-kuce daga al’umma a lokacin da Ganduje ya gabatar da masarautar a baya, wasu da yawa sun la’anta matakin.