Connect with us

Uncategorized

APC Tayi Babban Rashi A Yayin da Kotu ta Tabbatar da Zaben Tambuwal

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotun daukaka kara a ranar Juma’a, 22 ga Nuwamba, ta tabbatar da amince da zaben gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato.

Naija News ta gane da cewa kwamitin alkalai hudu wadda Mai shari’a Husseini Mukhtar ya jagoranta, sun dage da cewa an zabi Tambuwal ne bisa tsari kuma da dagewa kan hukuncin da kotun a baya ta yi na watsi da karar da aka shigar kan gwamnan daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma dan takarar gwamna, Ahmed Aliyu Sakkwato.

Kotun ta yanke hukuncin cewa wadanda suka gabatar da kara da zarge-zarge kan rashin amincewa da zaben sun kasa bayar da tabbacin zargin da su ke.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kotun daukaka kara wacce ke zaune a jihar Kaduna ta sallami wasu mambobi biyu a majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Talata.

‘Yan Majalisa biyun suna wakilci yankin Kagarko da Sanga bi ne a majalissar dokokin jihar Kaduna.