Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 22 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 22 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Majalisar dattijai ta amince da karuwar Kudin Haraji (VAT) daga 5% zuwa 7.5%

A ranar Alhamis din da ta gabata ne majalisar dattijan Najeriya, ta amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ta kara harajin kasa (VAT) zuwa kaso 7.5%.

Amincewa da yarjejeniyar wani bangare ne na gyare-gyare a cikin Dokar Kudi bakwai da na Majalisun Dokokin Kasar da suka shafi harajin da ake biya a kasar.

2. Kotu Ta Soke Nadin Masarauta Hudu da Ganduje Ya Kafa

A ranar Alhamis, 21 ga Watan Nuwamba 2019 ne wata babbar kotun jihar Kano ta soke nadi da kirkirar wasu masarauta guda hudu a jihar Kano.

Ku tuna Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano, ya mika Alkibba da Sandar Shugabanci ga sabbin Sarakai hudu da ya nada a Jihar.

3. Dino/Smart: INEC ta Sanar da Ranar Karshe Zaben Jihar Kogi

Hukumar Gudanar da Zaben Kasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 30 ga Nuwamba, don gudanar da zaben lashe kujerar Sanata a Yammacin Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa hukumar zaben ya tsaida ranar da za a gudanar da zaben ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar alhamis da yamma ta hannun Festus Okoye, kwamishina na kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Kwamitin Ilimin masu jefa kuri’a.

4. Kungiyar Amnesty International ta zargi Shugaba Buhari da tsoratar da ‘Yan Najeriya

Kungiyar Amnesty International a wata sanarwa ta zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da yin amfani da jami’an tsaro da kuma bangaren shari’a don tsananta wa ‘yan Najeriya.

Kungiyar yaki da haƙƙin ɗan Adam din ta bayyana hakan yayin da ta la’anci ci gaba da tsare jagoran ƙungiyar #RevolutionNow, Omoyele Sowore ta hannun ma’aikatar tsaro ta DSS.

5. Tsohon Gwamnan Neja, Talba ya Gargadi Hukumar INEC Akan Zaben Jihar Kogi

Bayan kusan mako daya da gudanar da zaben gwamnoni a Jihar Kogi da Bayelsa da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu-Babangida-Aliyu, ya yi kira ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta soke zaben.

A wata rahoto da Jaridar Vanguard ta rabbar wadda Naija News Hausa ta gano, Aliyu, tsohon gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP, ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da jami’in yada labaran sa, Bala Peter, ya fitar ranar Alhamis, 21 ga Nuwamba, a Minna, babban birnin Jihar Neja.

6. Kotu ta Yanke Hukuncin Kwace kudi har Miliyan N280M da ke da halaka da Invictus Obi

Wata Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta umarci Obinwanne Okeke, wanda aka fi sani da suna Invictus Obi da ya ba sadaukar da mallakarsa mai adadin kudi miliyan N280,555,010 ga Gwamnatin Tarayya.

Mai shari’a Rilwan Aikawa ne ya bayar da wannan umarnin a ranar alhamis biyo bayan gabatar da karar da mai ba shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), Rotimi Oyedepo ya bayar.

7. ‘Yan bindiga sun hari Kwamishinan a Jihar Oyo, da Kashe Direbansa

A ranar Laraba da ta wuce, wasu ‘yan hari da bindiga sun hari Kwamishinan filaye a jihar Oyo, Abdulraheem Abiodun, a yayin da suka kashe direbansa.

A cewar gidan talabijin na Channels, lamarin ya faru ne bayan darukan kwamishanan suka sauke shi a gidansa.

8. 2023: Tsohon Gwamnan Zamfara, Yarima Ya bayyana Shirin Fita Takarar Shugaban Kasa

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima, yayin da yake magana kan shugabancin Najeriya a shekarar 2023, ya ce watakila zai iya fita takara a matsayin shugaban kasa dubin kiraye-kirayen da amintattunsa suke yi da neman ya fita takara.

Naija News Hausa ta gane da cewa Yarima ya bayyana hakan ne a Gusau, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Najeriya, watau Pride FM, na jihar Zamfara.

9. Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da tsare-tsaren gwamnatin tarayyar Najeriya na karbo bashin Euro miliyan 500.

Wannan shirin ya bayyana ne daga bakin Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Clement Agba, a karshen taron FEC da ya gudana a ranar Laraba a Abuja wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Bisa ga bayaninsa, za a yi amfani da rancen ne don tallafawa masana’antu, samar da ayyukan yi, da kuma aikin gona kuma ana tsammanin zai samar da guraben ayyuka miliyan 1.2 a kasar.