Connect with us

Labaran Najeriya

Tsohon Gwamnan Neja, Talba ya Gargadi Hukumar INEC Akan Zaben Jihar Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan kusan mako daya da gudanar da zaben gwamnoni a Jihar Kogi da Bayelsa da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu-Babangida-Aliyu, ya yi kira ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta soke zaben.

A wata rahoto da Jaridar Vanguard ta rabbar wadda Naija News Hausa ta gano, Aliyu, tsohon gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP, ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da jami’in yada labaran sa, Bala Peter, ya fitar ranar Alhamis, 21 ga Nuwamba, a Minna, babban birnin Jihar Neja.

A cikin bayanin nasa ya bukaci gwamnatin kasar a jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumar INEC da su soke zabukan saboda tabbatar da zaman lafiya, ci gaban dimokiradiyya da adalci a kasar.

“Muna rokon INEC da gwamnati da ke kan mulki da su soke zabukan saboda bukatar zaman lafiya, ci gaban dimokiradiyya da adalci. Wannan matakin ya cancanta ne musanman don Salomi Acheju Abuh da sauran mutane da aka kashe a jihohin jihar Kogi da Bayelsa yayin zaben jihar da aka gudanar a Asabar da ta gabata” inji Ali Babangida.

Tsohon Gwamnan ya yi Allah wadai da kisan shugabar mata ta PDP a karamar Hukumar Wada Aro a jihar Kogi, watau Malama Salome Abuh, wacce ta kone kurmus a cikin gidanta sakamakon wasu ‘yan ta’addan siyasa da suka gudanar da mumunar matakin.

“A matsayinmu na ‘yan kasa wayayyu, mun lura da matukar damuwa cewa dukan abin da suka gudana a zaben gwamnoni a jihohin biyu, ya kasance ne da yiwa ‘yan kasa lalatar kayakin su, aka gudanar da mummunan zalunci da amfani da karfi ba bisa ƙa’ida ba.”

“Don haka muke watsi da sakamakon zaben guda biyun gaba daya. Gudanarwann da sakamakon zaben a cikin jihohin biyu ba tabbacin zabe bane mai adalci, wannan kuwa ya nuna raunana ga dimokiradiyya kasar,” in ji shi.