Connect with us

Uncategorized

APC: ‘Yan Zanga-Zanga Sun Mamaye Titi da Bukatar a Tsige Oshiomhole

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu masu zanga-zanga a ranar Juma’a (yau) sun bukaci a cire Adams Oshiomhole a matsayin sa na Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

A wasu hotuna da Naija News Hausa ta ci karo da su a wata labarai da aka bayar a Premium Times, an gano masu zanga-zangar dauke da rubuce-rubuce zuwa sakatariyar jam’iyyar APC na kasa.

Wasu daga cikin katunan suna da rubutu kamar haka, “Dole ne Oshiomhole Ya Tafi”, “Barawo” da dai sauransu.

Naija News ta kula da cewa masu zanga-zangar, akasarinsu matasa ne, amma a yayin da suke gudanar da zanga-zangar, wasu tarin ‘yan ta’adda matasa kuma sun fito daga wata hanya inda sakatariyar APC ta ke. Suka kuwa hari masu zanga zangar da jifan duwatsu da sanduna domin tarwatsa su.

Akalla mutum guda ya jikkata a tashin hankalin. Ko da shike ba wanda ya gane ko wanene ke tallafawa masu zanga-zangar, amma ana zargin cewa wasu shugabannin jam’iyyar ta APC ne tare da wasu gwamnonin jam’iyyar ke kokarin ficewar Mista Oshiomhole a shugabancin jam’iyyar.

KARANTA WANNAN KUMA; 2023: Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima Ya bayyana Shirin Fita Takarar Shugaban Kasa.