Connect with us

Uncategorized

Dino Melaye Ne Sanadiyar Kashe-kashe Da Aka Yi A Zaben Kogi – APC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin jihar Kogi ta zargi Sanata Dino Melaye da alhakin tashe-tashen hankula da ya afku a yayin hidimar zaben fidda gwani wadda aka yi a kwanan nan a jihar.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Yahaya Bello, Mohammed Onogwu ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a gidan talabijin na Channels ranar Lahadi da ta gabata.

Onogwu a cikin hirar ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar tana da shaidar bidiyo da zai bayar da tabbacin cewa Sanata Dino ne ke rarrabar da kudi a ranar zaben.

“Muna da bidiyo, shaidar inda shi Dino Melaye yake rarraba kudi a layin da ake jefa kuri’a.”

“Sakamakon rahotannin da masu sa ido daban-daban suka bayar a bayan zaben, an karshe da cewa hakika zaben gwamnan ya karshe da gaskiya.”

“Duk tashe-tashen hankula da suka faru a zabukan da suka gabata, Dan takaran, Sanata Dino Melaye ne ya ke da alhakin haka.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dan takarar All Progressives Congress, Smart Adeyemi zai yi takara da Dino Melaye a zaben cike gurbi wanda aka dage zuwa ranar 30 ga watan Nuwambam, kamar yadda Hukumar Zabe  ta sanar”.