Abin Takaici! Gobara Ya Kone Wata Shiyar Kwalejin Kimiyya ta Tarayya da ke Bauchi

Abin bakin ciki ne a ranar Lahadin da ta gabata ga daliban Kwalejin Kimiyya ta Tarayya da ke Bauchi, a lokacin da gobara ta tashi a kan dakin kwanan wasu daliban hade da wani dan jarida a kauyen Gwallameji.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana da cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 1:30 na rana a daya daga cikin dakunan da ke gidan Tinubu kafin ta bazu zuwa wasu dakuna.

Duk da kokarin mazauna da masu nuna juyayi, sun yi iya kokarinsu don ganin sun lafar da gobarar amma duk kokarinsu a banza ne.

A cewar wani mazaunin gidan, David Adenuga wani Dan Jarida da ke aiki a gidan Jaridar Nation ya ce yayin da yake ba da labarin abin da ya faru kamar mafarki ne a gare shi kuma ya rasa dukkan kayayyakinsa a wutar.

Ya kara da cewa lallai babu wutar lantarki a lokacin kuma har yanzu ba a san musabbabin barkewar lamarin ba. Ya ce wutar ta shafi dakuna tara yayin da ma’aikatar kashe gobara suka isa wajen da taimaka wajen kashe wutar daga yaduwa zuwa sauran dakuna.

A cewar wata ‘yan macce, daliba da gobarar ta shafa, ta ce ba ta san inda za ta fara ba, abin da za ta yi ko ta inda za ta kasance yayin da wutar ta ƙone dukkan takaddun ƙima da shaidar karatunta duka zuwa toka.

Wani wanda abin ta rutsa da shi, dan Jarida tare da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, Saheed Ola, ya ce kayan aikin nasa da sauran kayan masarufin sun tafi tare da wutar amma ya gode wa Allah kan rayuwarsa.

Wani shaidar gani da ido shi ma ya kara da cewa gas din dafa abinci da dalibai ke amfani da shi ya taimakawa wutar da yaduwar, yana mai cewa galibin dakunan suna dauke da ‘gas na dafa abinci’