Connect with us

Uncategorized

Hatsarin Motar Tirela dauke da Jakuna ya Kashe Mutane 12 a Jihar Sakkwato

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoton da ke isa ga Naija News Hausa ya bayyana mutuwar akalla mutane 12 sakamakon hatsarin mota da ya faru a Kasarawa a karamar hukumar Wamakko da ke jihar Sakkwato.

A cewar wasu shaidu, hadarin ya shafi wani motar tirela dauke da jakuna da kuma mutanen da aka ce sun fito ne daga karamar hukumar Rabah ta jihar.

Labarai ta bayyana da cewa motar na kan hanyar zuwa jihar Neja ne, a yayin fasinjoji ke kan zuwa kasuwancin su kamar yadda suka saba zuwa taimakawa mazauna garin su kwashe kayan amfanin gonarsu zuwa gidajensu daga gonaki.

An ce direban motar ya rasa kwanturon motar ne a yayin da motar ta fantsama kan titin da juya-juya. A nan take kuwa mutane suka mutu yayin da abokan aikinsu da yawa suka samu raunuka daban-daban.

Ko da shike dai an bayar da cewa an wadanda suka jikkatar an dauke su zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo da asibitin kwararru na Sakkwato, inda suke karbar magani.

KARANTA WANNAN KUMA; Ahmed Musa, Kyaftin din Super Eagles Ya Dauki Nauyin Biyan Kudin ‘Yan Makaranta 100.