Connect with us

Uncategorized

Kotu Ta Umarci EFCC da Dakatar da Gurfanar da Tsohon Janar na Kwastam, Dikko

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke babban birnin tarayya, Abuja ta nemi Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) da ta dakatar da tuhumar da ake wa tsohon Kwanturo Janar na Kwastam (CGC), Abdullahi Inde Dikko da laifin makircin kawar da wasu kudade yayin da yake kan ofishi.

A wata hukunci da aka yanke a ranar Litinin da ta gabata, Mai shari’a Nnamdi Dimgba ya amince da gardamar Dikko da ke cewa ba za a sake gurfanar da shi ba daga wata hukuma yayin da ya kai ga arjejeniya da Gwamnatin Tarayyar kasar, da Ministan Shari’a na Tarayya (AGF) da Darakta-Janar na Ma’aikatar Gwamnatin Jiha. (DSS) don mayar wa da gwamnati dala miliyan 8m.

Mai shari’a Dimgba ya ce tunda an tabbatar da cewa akwai irin wannan yarjejeniya tsakanin Dikko da gwamnatin, kuma Dikko ya kai ga cika nasa arjejeniyar ta hanyar biyan 1,576,000,000 da ƙari ga Gwamnatin Tarayya, ta hanyar asusun hukumar EFCC a Babban Bankin Najeriya (CBN). “Bai kuwa dacea a ce hukumar EFCC ko wata hukuma ta sake gurfanar da shi Dikko ba kan wannan laifin.