Labaran Najeriya
Manya Ga APC Na Yunkurin Neman Shugaba Buhari Da Sake Shugabanci A Shekara Ta 2023
Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta reshen jihar Ebonyi, Charles Enya, ya shigar da kara wanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin bai wa Shugaba Muhammadu Buhari damar tsayawa takara a karo na uku.
Enya, wanda ya kasance sakataren shirye shirye ga shugaba Buhari yayin babban zaben shekarar 2019, ya shigar da karar mai lamba (FHC/AI/CS/90/19) a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abakiliki, bisa rahoton da aka bayar a hannun jaridar Daily Trust.
Babban jigon APC din ya ce wa’adi sau biyu ga shugabanci kasa da kujerar gwamnoni bai dai dai ta ba.
Enya a cikin ya karar ya bukaci babban lauya na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da kuma na kasa baki daya, da su cire sharuddan tsarin mulki wadanda suka takaita zababbun shugabanni da gwamnoni zuwa wa’adi biyu kawai.
A cikin karar kuwa ya hada da sunan Mohammed Sani-Omolori, magatakardan majalisun kasa; Majalisar Dattawa da Malami.
Naija News ta ba da rahoton cewa Sashe na 137 (1) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya a 1999 (kamar yadda aka yi gyara) na Tarayyar kasar, ya tanada cewa;
“mutum bai cancanta da mukamin Shugaban kasa ba idan an zabe shi ga irin wannan ofishin a zabe biyu da suka gabata”. Yayin da sashi na 182 (1) (b) ya ce “ba wanda zai nemi kujerar gwamna idan an zabe shi a irin wannan mukaman a zabukan da suka gabata biyu”.
Dan jam’iyyar APC na neman yiwuwar rushe sassan biyu. A cewarsa; “wannan sashe na 137 (1) (b) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya, 1999 (kamar yadda aka gyara) ya takaita shugabani zuwa wa’adi biyu kawai na shekaru hudu a kowanne karo, dokar ba shi da wata ma’ana sabili da yanayin nuna wariya a cikin dangane da bangaren zartarwa da na majalisun dokoki a Najeriya, don haka babu komai a ciki kuma babu makawa ”.
Charles ya nemi “odar kotu da ta rushe da kuma kawar da sashe na 137 (1) (b) da 182 (1) (b) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya, 1999 (kamar yadda aka gyara a baya).”
KARANTA WANNAN KUMA; Kungiyar Amnesty International ta zargi Shugaba Buhari da tsoratar da ‘Yan Najeriya