Connect with us

Labaran Najeriya

Bello: Natasha Akpoti ta Aika wa Shugaba Buhari Gargadi akan zaben Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yar takarar kujerar gwamna a zaben 2019 na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi, Natasha Akpoti ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake yin la’akari da yanayin da ya shafi sakamakon zaben ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi.

Natasha a cikin gargadin ta bukaci Shugaba Buhari da ya binciki alamuran tashe-tashen hankula yayin zaben gwamna na Kogi da aka kamala a mako biyu da ta gabata.

Ta bukaci Shugaban kasar da ya umarci ‘Yan sanda su yi nazari da binciken zargin da ake wa Yahaya Bello, gwamnan jihar da kuma dan takara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yayin zaben, da cewa Gwamnan ya ba da umarnin a kashe ta.

Natasha ta gabatar da hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata, a sakon ta da ta wallafa a shafin Twitter inda ta rubuta:

“Ya Shugaba Buhari, na gode da bada umarnin gudanar da bincike kan kisan shugaban matan PDP, Malama Abuh, wadda ‘yan jam’iyyar APC suka yi a Kogi. Don Allah a umarci ‘yan sandan Najeriya da su binciki wannan hari da Yahaya Bello hadi da ‘yan ta’addan Jam’iyyar APC a Kogi suka gudanar a ya yi zaben jihar da aka kamala.”