Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Borno, Zulum Ya Tsige Shugaban Ma’aikatan Jihar, Mohammed Hassan

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamna Babagana Zulum na Borno ya kori shugaban ma’aikatar jihar (HOS), Mista Mohammed Hassan, daga nadin nasa.

Naija News ta fahimci cewa Alhaji Usman Shuwa, Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Talata a Maiduiguri, babban birnin Jihar.

Shuwa ya bayyana da cewa gwamnan ya kuma amince da nadin Mista Simon Malgwi, a matsayin sabon HOS, ya kara da cewa sabon nadin zai fara aiki ne ana take ba tare da wata jinkirta ba.

Sanarwan na kamar haka;

“Gwamna Babagana Zulum ya tsige Mohammed Hassan daga mukaminsa na HOS da gaggawa.

“Saboda haka ya amince da nadin Barrister Simon Malgwi, a matsayin sabon HOS,” in ji shi.

Shuwa ya kara da cewa har zuwa lokacin nadin sabon HOS Malgwi, shi ne Babban Magatakardar da kuma Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi.