Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 26 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 26 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Dokar Kalaman Kiyayya da Ta Kafofin Watsa Labaru Bai da wata Daraja Ga ‘yan Najeriya – Inji Wata Kungiya

Cibiyar Kula da Kare Hakkin Bil Adama da Ilimin ‘Yan Adam, yayin da take bayyana ra’ayinta game da jita-jitar kafofin watsa labarun da kuma maganganun kalaman nuna kiyayya, an lura cewa dokar ba za ta kara wani daraja ga alumma ba.

‘Yan Kungiyoyin sun bayyana kudirin da aka gabatar a zaman wani hari kan kundin tsarin mulki da ya ba da dama ga ‘yan kasa na fadin albarkacin bakin su.

2. 2023: Mafi yawan Shugabannin Kudancin Najeriya Matsorata Ne – Fani-Kayode

Ministan zirga-zirgar jiragen sama a karkashin Gwamnatin Goodluck Jonathan, Femi Fani-Kayode, ya bayyana wasu shugabannin daga yankin Kudancin Najeriya a matsayin matsoratai.

Tsohon ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman da mukaddashin shugaban kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, Alhaji Musa Liman Kwande ya yi, cewa ‘yan Arewa za su zabi kawai ne dan takarar shugaban kasa wanda asalinsa dan Arewa ne a zaben shugaban kasa na 2023, ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba.

3. Mompha Ya Saura Kulle A Cikin Kurkuku

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, a ranar Litinin din nan ta gurfanar da Ismaila Mustapha, wanda ake wa lakabi da Mompha da ake zargi da cin amana da zalunci a layin yanar gizo.

Naija News ta fahimci cewa an tuhume shi da aikata laifuka 14 da suka hada da cin amana a layin yanar gizo, kamar yadda EFCC ta bayar.

4. Fadar Shugaban Kasa ta Mayar da Martani Kan Motar Daukar Kudi Na Tinubu a Zaben Shugaban Kasa

Farfesa Itse Sagay, shugaban kwamitin ba da shawara ga shugaban kasa kan yaki da cin hanci da rashawa (PACAC) ya mayar da martani kan kiraye-kirayen da ake yi na binciken Asiwaju Bola Tinubu.

Idan za ka/ki iya tunawa, akwai kiraye-kiraye da cece-kuce da ake mai yawa na Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) don bincika wasu motar daukar kudi zuwa banki da aka gano suna shiga gidan Cif Tinubu a gabanin babban zaben na 2019 a kasar.

5. Jonathan Ya Sayar da Kujerar Gwamnan Bayelsa Zuwa Ga APC – Inji Wata Kungiya

An zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da cin amanar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna da ya gabata a jihar Bayelsa.

Wata kungiya, Kungiyar Dattawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta ce ta damu matuka game da matsayin Jonathan da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayin zaben da aka kamala a jihar Bayelsa.

6. Wani Lauya ya zargi Shugaba Buhari da rashin biyayya ga umarnin Kotun Koli 40 Tun daga shekarar 2015

An zargi Shugaba Muhammadu Buhari da gaza bin umarnin kotu a lokuta da dama tun bayan da ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2015.

Kolawole Olaniyan, mai ba da shawara a fannin shari’a ga kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ya yi zargin cewa Shugaba Buhari ya nuna “rashin ladabi ga bin doka da take hakkin dan Adam, yin watsi da alƙalai na Najeriya a aƙalla sau 40 tun daga shekarar 2015.

7. Gwamnatin Tarayya Ta Mayar da Martani Zargin Da Amurka Keyi Ga Allen Onyema

A karshe gwamnatin Najeriya ta mayar da martani game da badakalar dala miliyan 20 da aka yiwa shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyema.

Naija News ta tuna cewa a ranar Juma’a, 22 ga Nuwamba, 2019, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta tuhumi Onyema da yaudarar bankuna da kuma karkatar da wasu kudade.

8. Kotu Ta Umarci EFCC da Dakatar da Gurfanar da Tsohon Janar na Kwastam, Dikko

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke babban birnin tarayya, Abuja ta nemi Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) da ta dakatar da tuhumar da ake wa tsohon Kwanturo Janar na Kwastam (CGC), Abdullahi Inde Dikko da laifin makircin kawar da wasu kudade yayin da yake kan ofishi.

A wata hukunci da aka yanke a ranar Litinin da ta gabata, Mai shari’a Nnamdi Dimgba ya amince da gardamar Dikko da ke cewa ba za a sake gurfanar da shi ba daga wata hukuma yayin da ya kai ga arjejeniya da Gwamnatin Tarayyar kasar, da Ministan Shari’a na Tarayya (AGF) da Darakta-Janar na Ma’aikatar Gwamnatin Jiha. (DSS) don mayar wa da gwamnati dala miliyan 8m.

9. Dino Melaye Yayi Magana Game da Kauracewa Zaben Kogi

Tsohon dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya mayar da martani ga zargin da ake da cewa yana da shirin kauracewa babban zaben na ranar 30 ga Nuwamba.

Naija News Hausa gane da cewa Dan takarar jam’iyyar All Democratic Party ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Smart Adeyemi, yayin sake zaben da aka yi wanda aka gudanar a ranar 16 ga Nuwamba kafin a bayyana zaben a matsayin wanda bai yi daidai ba.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Naija News Hausa