Connect with us

Uncategorized

Wasu ‘Yan Bindiga Da Ba a San Da Su ba Sun Sace Wani Firist na Katolika A Enugu

Published

on

at

advertisement

Wasu ‘yan hari da bindiga da ba a san ko su waye ba a ranar Litinin sun sace wani firist na cocin Katolika, Reverend Uba Malachy Asadu a Nsukka, jihar Enugu.

An sace Fr Asadu ne a kan hanyar Imilike-Nsukka, a yayin dawowarsa daga taron majalissar Ikilisiyar wadda aka gudanar a babban Ikilisiyar da ke a Nsukka.

Don bada tabbacin sace malamin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu, Ebere Amaraizu, ya ce bayanai game da satar firist din har yanzu bai cika da haske ba tukuna.

Duk da haka, ya ce jami’an ‘yan sanda tun daga samun rahoton sace Malamin suka watsar da darukan tsaron don neman kubutar da firist din daga hannun ‘yan garkuwan.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta fahimci cewa sace Babban Firist din, Asadu, ya cika lambar firistoci guda tara na cocin Katolika da aka sace a jihar Enugu cikin watanni takwas a wannan shekara.

Ka tuna da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Kwalejin Queen Of Apostle Year Seminary, Rev. Fr. Arinze Madu, Imezi-Owa a Ezeagu, karamar hukuma a jihar Enugu.

Haka kazalika aka bada rahoton zargin Fulani makiyaya da watanni biyu da suka gabata, kan kashe Rev FR Paul Offu, Babban Firist na cocin Katolika na St. James, Babban Parish, Ugbawka, a Enugu.

KARANTA WANNAN KUMA; Kalli Yadda A Cikin Mintoci ake Canza Sufar Jiki Daga Baki Zuwa Fari da Sinadirai